'Yan Bindiga Sun Kai Mugun Hari Ana Tsaka da Ibada a Kaduna, Sun Kashe Mutane

'Yan Bindiga Sun Kai Mugun Hari Ana Tsaka da Ibada a Kaduna, Sun Kashe Mutane

  • Ƴan bindiga sun shiga coci guda biyu, sun kashe mutane a garin Bakinpah-Maro da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun sace mutane 30 ciki har da malamin coci a harin da suka kai ranar Lahadi da ta gabata
  • Rundunar ƴan sandan Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce tuni jami'an tsaro suka bazama domin ceto waɗanda aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Ƴan bindiga sun kai farmaki wuraren ibadar mabiya addinin kirista watau coci-coci a kauyen Bakinpah-Maro, ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun hallaka aƙalla mutum uku, sannan suka yi awon gaba da wasu da dama a harin.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, sun ceto mutum 20 da aka sace

Taswirar Kaduna.
‘Yan bindiga sun kashe mutum 3, Sun sace wasu 30 a sabon harin coci a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ganau sun ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi lokacin da ƴan bindiga masu yawa suka kutsa kai cikin cocin ECWA da cocin katolika da ke garin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kaduna: Maharan sun sace mutane 30

Rahoton Channels tv ya nuna cewa ƴan bindiga sun kai farmakin ne ana tsaka da ibadar ranar Lahadi, lamarin da ya firgita mazuana garin.

Tsohon shugaban karamar hukumar Kajuru, Cafra Caino, ya ce ‘yan bindigar sun sace mutane 30 ciki har da wani fasto, Bernard Gajera.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Ya ce ƴan bindigar sun kashe mutane uku sannan sun yi garkuwa da adadi mai yawa na mutanen da suka je ibada a cocin guda biyu.

Kakakin ‘yan sandan ya ce har yanzu ba a tantance adadin wadanda maharan suka yi awon gaba da su a harin ba, kamar yadda Punch ta kawo rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tashi bama bamai a ofishin ƴan sanda, an rasa rayuka

Ya ce ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro sun fara farautar ‘yan bindigar don kama su tare da ceto mutanen da suka sace cikin ƙoshin lafiya.

Sojoji sun kashe ƴan bindiga a Kaduna

Kuna da labarin sojoji sun hallaka ƴan bindiga huɗu, sannan sun kuɓutar da mutum bakwai da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna

Rahotanni daga mazuana yankin Kasangwai sun nuna cewa sojojin sun farwa ƴan bindigar ne a maboyarsu ta jeji ranar Litinin da ta gabata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262