‘Kowa na Talaucewa’ Malamin Addini Ya Tura Zazzafan Sako ga Bola Tinubu

‘Kowa na Talaucewa’ Malamin Addini Ya Tura Zazzafan Sako ga Bola Tinubu

  • Shahararren malamin addinin Kirista a birnin tarayya Abuja, Cardinal John Onaiyekan ya yi kira ga Bola Ahmed Tinubu
  • Cardinal John Onaiyekan ya ce matsin tattalin arziki da ake ciki a Najeriya yana mayar da al'umma talakawa a fadin ƙasar
  • A karkashin haka, Faston ya bukaci gwamnatin tarayya ta sake duba wasu tsare tsaren gwamnati domin saukaka rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FTC, Abuja - Wani malamin addinin Kirista a Abuja ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan halin tsadar rayuwa da al'ummar Najeriya ke ciki.

Cardinal John Onaiyekan ya ce yan Najeriya na fama da matsin tattalin arziki sosai a wannan lokaci.

Kara karanta wannan

'Za mu yi nasara duk da ana wahala,' Jigon APC kan zabe mai zuwa a Edo

Fasto Cardinal
Fasto ya bukaci gwamnati ta saukakawa talakawa. Hoto: @CardOnaiyekan
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Faston ya bukaci gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sake shiri domin kawo sauki kan tsadar rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto ya bukaci Tinubu ya sake tsare tsare

Fasto Cardinal John Onaiyekan ya ce akwai buƙatar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nazari kan wasu tsare tsaren da ya kawo a gwamnatinsa.

Cardinal John Onaiyekan ya bayyana cewa tsare tsaren sun jefa al'umma cikin mawuyacin hali wanda hakan zai saka a canza su.

Fasto ya ce kowa na talaucewa a Najeriya

Cardinal John Onaiyekan ya ce yanzu ba a bambance talaka da mai dama dama, kowa ya dauki hanyar talaucewa.

A karkashin haka ya bukaci hukumomi su gaggauta daukar mataki su kuma talakawa su cigaba da addu'a.

Onaiyekan ya ce za a iya ƙure talaka

Cardinal John Onaiyekan ya bayyana cewa akwai lokacin da mutane za su gaza hakuri a Najeriya saboda wanda yake jin yunwa bai san hakuri ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya sake soke tsarin Ganduje, ma'aikata aƙalla 4,000 za su bar aiki a Kano

The Guardian ta wallafa cewa Onaiyekan ya ce ba zai yiwu ana ba mutane hakuri ba amma su kuma shugabanni suna cigaba da fantamawa da dukiyar ƙasa.

Tinubu ya raba abinci ga talakawa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake daukar matakin karya farashin abinci a Nijeriya ta hanyar fitar da hatsi daga rumbun gwamnati.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce Tinubu ya bayar da umarnin fitar da ton 42,000 na kayayyakin abinci domin rabawa talakawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng