Rikici Ya Barke a Bauchi: Gwamnati Ta bukaci ‘Yan Sanda Su Tuhumi Sanatan APC

Rikici Ya Barke a Bauchi: Gwamnati Ta bukaci ‘Yan Sanda Su Tuhumi Sanatan APC

  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Bauchi, Barista Abubakar Bununu ya nemi 'yan sanda su titsiye Sanata Shehu Buba
  • Sanata Shehu Buba dai ya yi ikirarin cewa tawagar 'yan sa kan Bauchi sun kashe wani Abubakar Yahaya saboda ya na sana'ar gawayi
  • Sai dai gwamnatin Bauchi ta gargadi sanatan cewa sare itatuwa domin yin gawayi haramun ne, kuma maganar tana gaban jami'an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Gwamnatin Bauchi ta ce ba za ta ci gaba da nade hannuwa ta na kyale mutane suna sare bishiyoyi ba wanda hakan zai iya haifar da zaizaya da lalacewar kasa.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Barista Abubakar Bununu ya bayyana hakan yayin da ya ke martani ga zargin da Sanata Shehu Buba ya yi.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: Ya na murna ya tsere daga kurkuku, jami'an tsaro sun cafke shi

Gwamnatin Bauchi ta yi magana kan ikirarin Sanata Buba na jami'ai sun kashe masu sana'ar gawayi
Gwamnatin Bauchi ta kai karar Sanata Shehu Buba ga 'yan sanda. Hoto: @SenBalaMohammed, @Benking443
Asali: Twitter

Bauchi: Sanata ya zargi gwamnati da kisa

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Sanata Shehu Buba ya yi zargin cewa jami'an gwamnatin Bauchi sun kashe wani matashi Abubakar Yahaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto cewa Abubakar Yahaya, wanda mazaunin kauyen Zaranda ne da ke karamar hukumar Toro ta jihar, yana sana’ar sayar da gawayi.

Sanata Shehu Buba ya yi ikirarin cewa 'yan sa kan jihar bisa jagorancin wani Umaru Shayi ne suka kashe Abubakar saboda ya na sana'ar gawayi.

Gwamnati ta nemi a binciki Sanata Buba

A martanin da ya yi, Barista Abubakar Bununu ya nemi hukumomin tsaro da su gayyaci sanatan mai wakiltar Bauchi ta Kudu domin amsa tambayoyi kan batutuwan tsaron jihar.

“Ina so in sanar da Sanata Shehu Buba Umar cewa an haramta saran bishiyoyi domin yin gawayi a jihar Bauchi”.

- A cewar kwamishinan.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru, Gwamna Abba ya sakawa yarinyar da taimaka masa a zaben 2019

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kwamishinan ya ce ya kamata dan siyasa kamar Sanata Shehu Buba ya kasance mai tauna kalamansa kan abin da ya shafi tsaron jihar.

Zanga zanga ta barke a Bauchi

A wani labarin, mun ruwaito cewa zanga zanga ta barke a kauyen Zaranda da ke Bauchi bayan da aka ce jami'an gwamanti sun kashe Abubakar Yahaya.

Zanga-zangar ta barke ne a ranar Talata, 10 ga Satumbar 2024 inda matasa suka mamaye babban titin garin domin adawa da kisan masu sana'ar gawayi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.