Gwamnatin Borno ta haramta sayar da itace da gawayi a Maiduguri

Gwamnatin Borno ta haramta sayar da itace da gawayi a Maiduguri

- An yi bikin murnar ranar yanayi a duniya a jihar Borno

- Majalisar dinkin duniya ta zabi ranar 5 ga Yuni matsayin ranar tunawa da yanayi

- Gwamnatin Borno ta bayyana matakin da zata dauka wajen magance gurbacewan yanayi

Gwamnatin jihar Borno ta haramta sayar da gawayi da itace a titunan Maiduguri, birnin jihar kuma ta baiwa yan kasuwa kwanaki biyu su koma kasuwar dake titin Damboa.

Gwamnatin ta dau wannan mataki ne domin dakile sare bishiyoyin da ake yi.

Antoni Janar kuma kwamishanan shari'ar Borno, Kaka-Shehu Lawan, ya bayyana hakan a wajen taron murnar zagayowar ranar yanayi a Maiduguri, rahoton Daily Trust.

Ya bayyana cewa an tura jami'ar tsaron gandun daji domin hana sare bishiyoyi kuma ana kokarin ganin yadda za'a shuka sabbin bishiyoyin da yan ta'ada suka lalata.

A cewar kwamishanan, an sare bishiyoyi milyan daya a fadin jihar.

KU KARANTA: Amurka tayi Alla-wadai da haramta Tuwita a Najeriya da Buhari yayi

Gwamnatin Borno ta haramta sayar da itace da gawayi a Maiduguri
Gwamnatin Borno ta haramta sayar da itace da gawayi a Maiduguri Hoto: Governor of Borno
Asali: Facebook

DUBA NAN: Najeriya za tayi sabbin jiragen yaki 20 a shekarar nan, Hukumar NAF

Gwamna Zulum wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Usman Umar Kadafur ya bayyana cewa an shirya taron ne domin wayar da kawunan mutane kan illar da ake yiwa yanayi.

Kadafur ya ce kawo yanzu an shuka iri na 5,000 kuma za'a shuka 500,000 a wurare daban-daban dake fadin jihar.

A bangare guda, mai girma gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da wasu gidaje 580, wadanda nan take a raba wa wadanda suke sansanin gudun hijira.

Jaridar Leadership ta fitar da rahoto cewa wadanda suka amfana da wadannan gidajen, su na rayuwa ne a sansanin gudun hijira na tsawon shekaru.

Farfesa Babagana Umara Zulum ya gina gidajen ne a garin Auno, karamar hukumar Konduga, inda aka yi gajeren biki kafin a rabawa talakawa gidajen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng