Bikin Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Dage Ranakun Komawa Makaranta a Karo na 2

Bikin Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Dage Ranakun Komawa Makaranta a Karo na 2

  • Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ba da hutun Mauludi domin tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW)
  • Ma'aikatar ilimi ta jihar ce ta bayyana hakan yayin da ta ke sanar da canja ranakun da za a bude makarantun fimare da sakandare
  • Kwamishinan ilimin Kano, Alhaji Umar Doguwa ya ce za a fara karatu a makarantun gwamnati na kudi a ranar 17 ga Satumba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta sake sauya ranakun bude makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar.

Gwamnati ta canja ranakun ne biyo bayan ayyana ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024, a matsayin ranar hutu na bukukuwan Mauludi.

Kara karanta wannan

Badakalar N440m: ICPC ta dura kan kakakin majalisar Kano da wasu mutane 4

Gwamnatin Abba Yusuf ta sanar da sabuwar ranar da daliban jihar za su koma makaranta
Gwamnatin Kano ta dage ranar da dalibai za su koma makaranta saboda Mauludi. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Kano: An sauya ranakun bude makarantu

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa daga Daraktan wayar da kan jama’a a ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, inji rahoton Leadership.

Sanarwar ta kara da cewa, an sanya ranar da dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu za su fara karatu zuwa Talata 17 ga Satumba, 2024.

Sai dai kuma sanarwar ta ce ɗalibai a makarantun kwana za su koma ne a ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024, kwana daya kafin a fara karatu.

Sanarwar ta yi nuni da cewa, an yi wannan gyara ne domin baiwa dalibai damar gudanar da bukukuwan Mauludin na tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

An taya al'ummar murnar Mauludi

Kwamishinan ilimi na jihar, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa:

“Mun yi wannan gyara ne domin baiwa dalibai damar gudanar da bukukuwan wannan rana mai alfarma, wadda ke nuna maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW)."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta sanya sabuwar ranar komawa makarantu, ta ba iyaye shawara

Da yake taya al’ummar musulmi murnar zagayowar wannan rana, kwamishinan ya bukaci jama’a da su rungumi dabi’ar hakuri, sadaukarwa, da kishin kasa.

Kwamishinan ya kuma tunatar da iyaye sababbin ranakun komawa makaranta, inda ya bukace su da su tabbatar da bin ka’ida domin kaucewa kawo cikas a kalandar karatu.

Abba ya sanya ranar biyan N70000

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta sanya lokacin da za ta fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi karancin albashi na N70,000.

Gwamna Abba Yusuf ya sha alwashin cewa gwamnatin Kano ce za ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin inda ya yiwa ma'aikata albishir.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.