Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar hutun bikin Mauludi

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar hutun bikin Mauludi

- Lokacin murnar bukukuwan Mauludi na wannan shekarar ya sake zagayowa

- Al'ummar Musulmai kan gudanar da bukukuwa domin nuna murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad

- Domin taya Musulmai murnar zagayowar wannan muhimmiyar rana, gwamnatin tarayya ta kan bayar da hutun aiki na kwana daya

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba, a matsayin ranar hutu domin gudanar da bikin Mauludi (Eid-El-Maulud) da Musulmai ke yi domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad.

Ministan ma'aikatar harkokin ciki gida, Rauf Aregbesola, ne ya sanar da hakan amadadin gwamnatin tarayya, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mohammed Manga.

Manga, darektan yada labarai da hulda da jama'a a ma'aikatar harkokin cikin gida, ya fitar da sanarwar ne da yammacin ranar Talata.

KARANTA: Zanga-zanga: FG ta ci tarar manyan gidajen talabiijin uku saboda kunyata gwamnati

A sakonsa na taya murna ga al'ummar Musulmi, Aregbesola ya bukaci su yi koyi tare da rungumar kyawawan halaye irin na Annabi Muhammad.

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar hutun bikin Mauludi
Bikin Mauludi a jihar Bauchi
Asali: Twitter

A cewarsa, yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin kasa.

Aregbesola ya roki 'yan Najeriya, musamman Musulmai, da su kaucewa duk wata halayya ta karya doka da tayar da tarzoma a kasa a irin wannan lokaci da wasu batagari ke cigaba da tafka barna.

KARANTA: An kashe jami'in kwastam a jihar Jigawa, an gudu da bindigarsa da ta abokinsa

Ministan ya bayyana cewa Nigeria ce alfaharin duk wani bakin mutum, a saboda haka akwai bukatar ta samu shugabanci da zai tabbatar da cigaban nahiyar Afrika da bakaken mutane.

Kazalika, ya bukaci Musulmai su hada kai tare da kauracewa duk wani abu da zai raba kansu.

Da ya ke magana a kan matasa, Aregbesola ya bukaci su bawa gwamnatin shugaba Buhari hadin kai a kokarin da take yi na gina musu kasa mai karfi da kowa zai kasace mai alfahari da ita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel