Girma Ya Fadi: Basarake Ya Shiga Matsala, ana Zarginsa da Sace Matashi da Karbar N2.5m
- Wani basarake a jihar Enugu ya shiga matsala bayan zargin yin garkuwa da matashi saboda filin gado
- Ana zargin Ezineso Oduma, Igwe Daniel Okechukwu Njoku da dauke matashi, Michael Njoku da karbar N2.5m
- Iyalan matashin sun roki gwamnatin jihar Enugu da hukumar tsaro ta DSS ta hukunta basaraken kan boye Michael
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Enugu - Wasu iyalai a jihar Enugu sun zargi basarake da garkuwa da dansu a jihar tun a watan Mayun 2023.
Iyalan na zargin basarake a Ezinesi Oduma, Igwe Daniel Okechukwu da karbar N2.5m daga gare su.
Ana zargin basarake da garkuwa a Enugu
Daya daga cikin iyalan, Charles Njoku shi ya tabbatar da haka inda ya ce an sace matashin tun a watan Mayun 2023, kamar yadda Legit ta samu.
Ana zargin basaraken ya dauke Michael Njoku a ranar 25 ga watan Mayun 2023 saboda iyalan sun ki sallama filin gado gare shi.
Iyalan suka ce basaraken ya karbi N25,000 na mai da N2m na jami'an tsaro sai kuma N350,000 lokuta daban-daban.
Har ila yau, suka ce suna bin umarnin ne saboda tsoron kada matashin ya rasa ransa sanadin bijirewarsu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa duk da biyan kudin, iyalan sun gagara sanin inda Michael yake ko yana cikin koshin lafiya.
Iyalan matashi sun roki gwamnatin Enugu
Basaraken ya yi ikirarin cewa lamarin na ofishin hukumar tsaro ya fararen kaya wato DSS reshen jihar Enugu.
Daga bisani, iyalan Michael sun roki gwamnatin jihar Enugu da Sifetan yan sanda da DSS domin hukunta basaraken.
Sai dai duka wannan zargi ne saboda jaridar Legit ba ta da tabbaci kan haka duba da har yanzu ba a tabbatar da zargin iyalan matashin a kotu ba.
Enugu: Yan bindiga sun hallaka shugaban kasuwa
Kun ji cewa Ƴan bindiga sun yi ta'asa a jihar Enugu a wani harin da suka kai a ƙaramar hukumar Enugu ta Kudu.
Miyagun ƴan bindigan sun hallaka shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar Ogbete yayin harin da suka kai da tsakar dare.
Ƴan bindigan sun hallaka Stephen Aniagu ne a ranar Asabar bayan sun bi sawunsa lokacin da yake kan hanyar komawa gida.
Asali: Legit.ng