Ambaliya: Majalisar Dinkin Duniya Ta Bayyana Tallafin da Za Ta Kaiwa Mutanen Maiduguri
- Majalisar Dinkin Duniya ta ziyarci Maiduguri, babban birnin jihar Borno domin duba mummunar ambaliyar ruwa da ta afku
- Bayan duba irin barnar da ambaliyar ta yi, Majalisar Dinkin Duniyar ta ce akwai bukatar a kaiwa wadanda abin ya shafa agajin gaggawa
- Tawagar majalisar da kungiyoyin agaji sun ta yi samar da abinci, ruwan sha mai tsafta, da matsuguni ga wadanda ambaliyar ta shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Jami’ai daga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji sun ziyarci Maiduguri domin duba mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa yankin.
Tawagar ta kunshi kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa karkashin jagorancin kodinetan ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mohamed Fall.
Majalisar Dinkin Duniya ta je Borno
Sun isa babban birnin jihar Borno ne a ranar Asabar domin tantance barnar da ambaliyar ta yi sakamakon fashewar madatsar Alau, inji rahoton Channels TV.
Jami’in yada labarai na cibiyar yada labaran Majalisar Dinkin Duniya, Oluseyi Soremekun ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ranar Lahadi.
Soremekun ya ce tawagar ta gana da mazauna yankin da abin ya shafa, da jami’an gwamnati, da kuma gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum.
Majalisar Dinkin Duniya ta magantu
Sanarwar ta ce bayan tantance irin barnar da aka yi ne tawagar ta kuma bayyana matakan tallafin gaggawa da ya kamata a kai wa wadanda iftila'in ya shafa.
“Mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa na fuskantar tashin hankali a wannan lokaci, saboda ambaliyar ta faru ne a lokacin da ake fama da matsananciyar rashin abinci.
“Na ga irin barnar da ambaliyar ta haifar, da kuma lalata gidaje, kasuwanci, da kayayyakin more rayuwa. Na kuma ga yadda al’ummar da abin ya shafa ke shan wahala.”
- A cewar Mohamed Fall.
Tawagar ta yi alkawarin daukar matakai cikin gaggawa domin rage radadin da iyalan da suka rasa matsugunansu ke ciki, ta hanyar samar da abinci, ruwan sha mai tsafta, da matsuguni.
Abin da ja jawo ambaliyar Maiduguri
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar raya Arewa maso Gabas ta dora alhakin fashewar madatsar Alau ga rashin kargon gini da cunkushe wanda ya jawo ambaliyar Maiduguri.
Sai dai kuma, babban daraktan gudanarwa da harkar kudi na hukumar NEDC, Garba Iliya ya ce a halin yanzu an ba da kwangilar gyara madatsar ruwan.
Asali: Legit.ng