Matakin NNPC Ya Jefa Tinubu a Matsala: SERAP Ta Maka Gwamnatin Tarayya a Kotu

Matakin NNPC Ya Jefa Tinubu a Matsala: SERAP Ta Maka Gwamnatin Tarayya a Kotu

  • Kungiyar kare hakkokin tattalin arziki da tattalin arziki (SERAP) ta maka Shugaba Bola Tinubu a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja
  • Kungiyar SERAP ta shigar da Tinubu da ministan shari'a, Mista Lateef Fagbemi da kuma NNPCL kan karin kudin man fetur
  • SERAP ta bukaci kotun da ta tirsasa Shugaba Tinubu ya janye karin kudin fetur da kuma umartar Fagbemi ya binciki kamfanin NNPCL

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kare hakkokin tattalin arziki da tattalin arziki (SERAP) ta maka Shugaba Bola Tinubu a gaban kotu.

An ce SERAP ta yi karar Tinubu ne bayan da ya gaza janye karin kudin man fetur da NNPCL ya yi da kuma gaza bincikar kamfanin man.

Kara karanta wannan

"Mun damu da halin da a ke ciki": Shugabannin APC sun shirya ganawa da Tinubu

SERAP ta yi karar Shugaba Tinubu kan karin kudin man fetur
SERAP ta yi karar Tinubu, ministan shari'a da NNPCL a gaban babbar kotu. Hoto: @SERAPNigeria
Asali: Twitter

Kungiyar SERAP ta sanar da shigar da karar ne a shafinsa na X a ranar Lahadi, 15 ga watan Satumbar 2024.

SERAP ta maka Tinubu a kotu

Wadanda SERAP ta shigar da karar sun sun hada da babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a, Mista Lateef Fagbemi da kuma NNPCL.

A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1361/2024 da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja, SERAP na neman kotun:

“Ta tirsasa Shugaba Tinubu ya umurci NNPC ya janye karin farashin man fetur da ya yi zuwa N845 daga N600, wanda ya sabawa kundin tsarin mulki.”

A cikin karar, SERAP ta na jayayya cewa:

Ƙaruwar farashin man fetur ya na haifar da wahala ga waɗanda ba su da wadata. A yayin da tattalin arzikin kasar ke kara tabarbarewa, karin kudin man zai jefa mutane a talauci."

Kara karanta wannan

Bayan sako shugaban NLC, hukumar DSS ta bayyana dalilin kai samame ofishin SERAP

Dalilin SERAP na zuwa kotu

Jaridar Vanguard ta rahoto SERAP ta kuma bukaci kotun da ta:

“Tilastawa Shugaba Tinubu ya umarci Mista Lateef Fagbemi, da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da su binciki zarge-zargen cin hanci da rashawa a NNPC.
"Binciken zai hada da zargin kashe $300m da aka karbo na ‘kudin bailout’ daga gwamnatin tarayya a Agustan 2024, da kuma $6bn da masu shigo da fetur ke binta bashi."

SERAP na neman kotun:

“Tilasta tirsasa Shugaba Tinubu ya umarci Lateef Fagbemi da hukumomin yaki da rashawa da su gurfanar da duk wanda ake zargi da hannu wajen almundahana a NNPCL.

DSS ta kai samame ofishin SERAP

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar SERAP ta zargi hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da kai samame hedikwatarta da ke Abuja ba bisa ka'ida ba.

SERAP ta zargi DSS da kai samamen ne awanni kadan bayan da ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya ba da umarni a binciki NNPCL kan zargin almundahana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.