Yadda Tafiye Tafiyen Remi Tinubu Suka Lakume N700m a Cikin Wata 3
- Uwargidan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta gudanar da tafiye-tafiye zuwa ƙasashe biyar a cikin watanni uku
- Gwamnatin tarayya ta kashe N701m saboda tafiye-tafiyen da Remi Tinubu ta yi zuwa ƙasashen wajen a tsawon wannan lokacin
- Haka kuma, gwamnati ta kashe N314m saboda wasu shirye-shirye guda shida da uwargidan shugaban ƙasan ta gabatar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta kashe maƙudan kuɗaɗe domin tafiye-tafiyen uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu.
A cikin watanni uku gwamnatin tarayya ta kashe kimanin N701m domin ɗaukar nauyin tafiye-tafiyen da Remi Tinubu ta yi zuwa ƙasashe biyar.

Asali: Facebook
Jaridar The Punch ta ce ta gano hakan ne ta amfani da manhajar Govspend, wacce ke bin diddigin yadda gwamnatin tarayya take kashe kuɗaɗe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta kashe kuɗi kan Remi Tinubu
Bayanan sun nuna cewa gwamnatin ta biya Naira miliyan 700,707,532 a tsawon watanni uku, saboda tafiye-tafiyen da Remi Tinubu ta yi zuwa ƙasashe biyar, ciki har da ƙasashe biyu na Afirika.
A ranar 17 ga watan Nuwamba, 2023, gwamnati, ta asusun gidan gwamnati ta fitar da kudi N77,659,888 domin siyan dala ($94,314) saboda ziyarar Remi Tinubu zuwa ƙasar Amurka.
A ranar 24 ga watan Fabrairu, 2024, gwamnati, ta asusun gidan gwamnati ta biya N149,794,284 domin siyan dala ($152,831) saboda ziyarar uwargidan shugaban ƙasan zuwa Faransa a ranar 4 ga watan Janairu, 2024.
A ranar 15 ga watan Maris, 2024, gwamnati ta biya N202,386,198 ta asusun gwamnati domin siyan dala ($126,834) saboda tafiyar Remi Tinubu zuwa ƙasar Mozambique a wannan watan.
A wannan ranar kuma, gwamnati ta biya N144,571,785 domin siyan dala ($96,118) saboda ziyarar uwargidan shugaban ƙasan zuwa Addis Ababa a ƙasar Habasha, a ranar 9 ga watan Fabrairu, 2024.
Gwamnati, ta hanyar asusun ajiya na gidan gwamnati, ta biya N126,295,377 domin siyan dala ($83,967) saboda tafiyar Remi Tinubu zuwa birnin Landan a wannan watan.
Shirye-shiryen Remi Tinubu sun ci kuɗi
Bugu da ƙari, gwamnati ta kashe jimillar kuɗi N314,231,472 a kan shirye-shirye shida na uwargidan shugaban ƙasan cikin watanni huɗu.
Hakan na nuni da cewa gwamnati ta kashe jimillar kuɗi N1,014,939,004 wajen tafiye-tafiye da shirye-shiryen uwargidan shugaban ƙasa a cikin tsawon watanni bakwai.
Remi Tinubu ta goyi bayan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa uwargidan Shugaba Bola Tinubu, Oluremi Tinubu ta bayana cewa shugaban ƙasanya na duk mai yiwuwa domin inganta Najeriya.
Uwargidan shugaban ƙasan ta ce a kullum ƙoƙarin Tinubu shi ne yadda zai kawo sauyi a ƙasar nan fiye da yadda ta ke a halin yanzu.
Asali: Legit.ng