Hon. Aliyu Garu: ‘Dan Majalisar da Matarsa ta Raba Sandunan Rake a Matsayin Tallafi

Hon. Aliyu Garu: ‘Dan Majalisar da Matarsa ta Raba Sandunan Rake a Matsayin Tallafi

  • Sunan Aliyu Aminu Garu ya na yawo yanzu a shafukan sada zumunta saboda matarsa ta raba sandunan rake
  • Mai dakin ‘dan majalisar tarayyar ta ba mutane rake a matsayin tallafi wanda hakan ya jawo kakkausan suka
  • Kafin wannan abin da ya faru, Aliyu Aminu Garu ya saba ba mutanen mazabarsa tallafin miliyoyin kudi a Bauchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bauchi - A kokarin ta taimaki jama’a, mai dakin Aliyu Aminu Garu ta jawo masa matsalar da za ta iya yi masa lahani a tafiyar siyasa.

Hon. Aliyu Aminu Garu shi ne mai wakiltar mutanen mazabar garin Bauchi a majalisar wakilan tarayya a karkashin jam’iyyar PDP.

Rake.
Matar 'dan majalisar Bauchi, Hon. Aliyu Aminu Garu ta raba sandunan rake Hoto: Abdulrahman Sanusi.
Asali: Facebook

Kamar yadda aka samu bayanai daga shafin Order Paper, wannan ne karon farko 'dan siyasar mai shekara 62 ya zo majalisar wakilan kasa.

Kara karanta wannan

Halilu Buzu: Yadda mugun ‘dan bindiga ya gamu da ajali da ya fada tarkon sojoji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar 'dan majalisar Bauchi ta raba rake

Kwanan nan hotuna su ka rika yawo inda aka ga matar Hon. Aliyu Aminu Garu ta fito ta na rabawa bayin Allah wasu sandunan rake.

An ce wannan mata ta yi haka ne da nufin tallafawa jama’a su samu jarin kasuwanci ta hanyar saida rake a mazabarsu da ke Bauchi.

A maimakon a tafawa matar ‘dan siyasar, jaridar Aminiya ta ce hakan suka kurum ya jawo a wajen ‘yan adawa da masu bin labarai.

Tallafin Aliyu Aminu Garu a majalisa

Sai dai duk da wannan hayaniya da ake yi, Legit Hausa ta samu labarin yadda Aliyu Aminu Garu yake taimakawa al’ummarsa a garin Bauchi.

Kwanaki gwamnatin jihar Bauchi ta ce ‘dan majalisar ya raba kudi da takin zamani na N85m ga mata, matasa, marasa galihu da manoma.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe mai gidan Bello Turji da wasu jiga jigan yan ta'adda

A karkashin tsarin Ali Garu, ‘dan majalisar ya ba da kyautar buhunan taki 600 kuma ya raba kudi domin ragewa talakawa radadin rayuwa.

‘Dan majalisar ya ba da tallafin karatu da gudumuwar bukukuwa kuma ya ba wani daga cikin magoya bayansa kyautar sabon abin hawa.

Kamar yadda aka yi wa wasu 'yan siyasa tabo da rakumi, rediyo zuwa makara, wannan rake da da aka raba za su iya bin 'dan majalisar.

Rake: Jam'iyyar PDP ta soki 'dan majalisa

Yanzu da ake kukan tsada da kuncin rayuwa, ‘yan adawa sun samu abin hamayya, an ji labari jam'iyyar PRP ta caccaki matar Aliyu Garu.

Wani sakataren jam'iyyar hamayyar ya ce bai kamata a yau a ga ana rabon rake da sunan tallafin kasuwanci ba, ya ce hakan abin kunya ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng