Sojoji Sun Kashe Mai Gidan Bello Turji da Wasu Jiga Jigan Yan Ta’adda

Sojoji Sun Kashe Mai Gidan Bello Turji da Wasu Jiga Jigan Yan Ta’adda

  • Rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara kan yan bindiga masu garkuwa da mutane a yankin Arewacin Najeriya
  • An samu labarin cewa rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar hallaka mai gidan Bello Turji, Kachalla Halilu Sububu a safiyar yau
  • Haka zalika sojojin Najeriya sun hallaka wasu jiga jigan yan bindiga a yankin Arewa ta yamma bayan farmaki da suka kai musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Rundunar sojin Najeriya ta sanar da samun nasarar kashe wasu manyan yan ta'adda a Arewa ta Yamma.

An ruwaito cewa cikin wadanda aka kashe akwai Kachalla Halilu Sabubu wanda ya kasance mai gida ne ga Bello Turji.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi mutane a Arewa

Sojoji
Sojoji sun kashe babban dan bindiga a Zamfara. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da hadimin shugaba Bola Tinubu, Abdulaziz Abdulaziz ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kashe mai gidan Bello Turji

BBC Hausa ta wallafa cewa rundunar sojin Najeriya ta kashe mai gidan Bello Turji, Kachalla Halilu Sububu.

Rahotanni sun nuna cewa a yau Juma'a, 13 ga Satumba ne aka kashe ƙasurgumin ɗan bindigar da ya addabi Arewa.

Wannan na cikin nasarori da rundunar sojin Najeriya ta fara samu a kan yan ta'adda tun bayan tarewar wasu shugabannin tsaro a Arewa ta Yamma.

Sojoji sun kashe jiga jigan yan ta'adda

Bayan kashe Halilu, sojojin sun yi nasarar kashe Kachalla Ali Kawaje wanda ya taba harbo jirgin soja a Kaduna.

Haka zalika sojojin sun kashe Baleri wanda shi ne ya taba sace dalibai masu yawa a jihar Kaduna kafin ya koma yankin Zamfara.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da ƴan sanda sun mamaye fadar Sarki bayan fara raɗe raɗin ya rasu

Cikin wadanda aka kashe akwai Damina, Modi-Modi, Dangote da sauran manyan barayi masu garkuwa da mutane a Zamfara.

Matasa sun tsere daga wajen Turji

A wani rahoton, kun ji cewa wasu matasan garin Moriki aZamfara sun kubuta daga hannun babban dan ta'adda, Bello Turji bayan ya yi musu barazanar kisa.

Bello Turji ya yi holon matasan a wani bidiyo yana cewa idan ba a kawo masa kudin fansa ba zai kashe su kamar yadda aka yi wa Sarkin Gobir.

Sai dai duk da haka akwai wasu mata guda shida a hannun dan ta'addar daga garin Moriki duk da cewa bai yi musu barazanar kisa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng