'Yan Sandan Kaduna Sun Tare Miyagun 'Yan Bindiga a Hanya, An Nakasa Masu Mugun Nufi
- Rundunar yan sandan Kaduna ta bayyana samun nasara kan gungun yan fashi da yan ta'addan da ke shirin kai hari
- Rundunar ta ce an samu nasarar bayan bibiyar wasu muhimman bayanai kan wurin da yan ta'addan su ke, tare da kai masu samame
- A musayar wuta da aka dade ana yi, yan sandan sun yi nasarar kama dan bindiga da wasu mugayen yan fashi, hadi da kashe mutum guda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Rundunar yan sanda a Kaduna ta yi nasarar fatattakar wasu bata-gari da su ka hada da yan bindiga da yan fashi a jihar.
Jami'an hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, ASP Mansur Hassan ne ya tabbatar da nasarar ta su a sanarwar da ya fitar ranar Alhamis.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa jami'an yan sanda sun samu rahotannin sirri kan ayyukan bata-garin kafin su yi nasarar kama su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kama yan ta'adda a Kaduna
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa dakarun yan sandan Fushi Kada a Kaduna sun kai samame yankin Karji/Sabon Tasha inda su ka yi gaba da gaba da yan ta'adda.
A nan ne aka fafata har aka yi nasarar kama bata-gari guda shida, tare da illata wani Christopher Bobai da aka fi sani da Baban Dodo, wanda ya mutu daga baya.
Kaduna: Abin da aka kwace daga yan ta'adda
Yan sanda a jihar Kaduna sun kwace bindiga kirar Turai da wata hadin gida, sai kayan sojoji, adduna uku, takalman shiga daji kafa hudu daga hannun yan ta'adda.
Sauran kayan amfanin 'yan ta'addan da aka yi nasarar kwace wa sun hada da layukan waya guda shida, bakaken kaya guda biyu da huluna guda biyu.
Sojoji sun hallaka yan ta'adda a Kaduna
A wani labarin kun ji cewa dakarun sojojin kasar nan sun shiga dajin da ke karamar hukumar Kagarko a Kaduna inda su ka ragargaza yan ta'adda.
Mazauna yankin sun ce mafarauta ne su ka jagoranci sojojin inda aka samu damar ceto wasu mutum bakwai da aka yi garkuwa da su a cikin dajin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng