Yunwa: Wasu Gwamnonin Jihohin Kudu Sun Fitar da Tsarin Wadata Jama'a da Abinci
- Gwamnoni shida da ke Kudu maso Yamma sun kammala shirya yadda za a wadata mazauna yankin da abinci
- Sun cimma matsayar ne a jihar Legas bayan an gudanar da muhimman taruka hudu daga watan Yuni zuwa yanzu
- Daraktan shirin ci gaban Yammacin Najeriya, Seye Oyeleye ya ce za su aiwatar da shirin a kungiyance da kuma daidaiku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Gwamnonin Kudu maso Yammacin kasar nan sun sake hallara a jihar Legas inda su ka kammala fitar da matsaya kan magance yunwa a yankin.
A sanarwar da daraktan shirin ci gaban yankin, Seye Oyeleye ya fitar, ya ce sun shirya tsaf kan yadda za a girbe amfanin gona da adana su saboda jama'a.
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa a taron da aka gudanar a Legas, karkashin jagorancin gwamna Babajide Sanwo-Olu, an yaba da kokarin gwamnatin tarayya kan wadata kasa da abinci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin Kudu maso Yamma sun hada kai
Kungiyar gwamnonin Kudu maso Yamma ta umarci kwamishinonin noma a jihohi shida da ke yankin su gaggauta zama domin duba tsarin samar da abinci da aka fitar.
Taron zai biyo ganawar da gwamnonin yankin su ka rika yi tun a watan Yuni, a wani yunkuri na nemo hanyoyin alkinta amfanin gonakin da za a samu.
Jihohin Kudu maso Yamma sun yi shiri
Shirin ci gaban Yamma a Najeriya ya bayyana cewa kowace jiha shida a yankin ta kammala shirya bayanan matakan samun wadatar abinci.
Daraktan shirin, Seye Oyeleye ya bayyana cewa jihohin sun aiko da daftarin shirye-shiryensu, kuma za a mika jawaban ga shugaban kungiyar gwamnonin yankin.
Abinci: Gwamnan Kudu maso Yamma ya dauki mataki
A baya mun ruwaito cewa gwamnan Ogun, Dapo Abiodun ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da kara farashin abinci ba bisa ka'ida a jiharsa ba domin ana jin jiki.
Gwamnan ya kuma bayyana dakatar da karbar haraji daga yan kasuwannin da ke jihar, a daidai lokacin da ya ce ana shirin bijiro da tsarin kayyade farashin kayan abinci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng