Magidanci Na Neman Matarsa da Ƴaƴansa 5, Ana Fargabar Sun Bace a Ambaliyar Maiduguri

Magidanci Na Neman Matarsa da Ƴaƴansa 5, Ana Fargabar Sun Bace a Ambaliyar Maiduguri

  • Ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri a jihar Borno a ranar Litinin ta yi barnar da ba a taba gani ba a shekaru 30 da suka gabata
  • Wadanda suka tsira sun ba da labarin abubuwan da suka faru da su yayin da kungiyoyin agaji ke aikin ceto wadanda suka makale
  • Wani magidanci da ya tsira, ya koka kan cewa har yanzu bai san inda matarsa da ƴaƴansa biyar suke ba tun bayan faruwar ambaliyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Wadanda suka tsira daga ambaliya ruwa a Maiduguri, mafi muni a cikin shekaru 20, sun ba da labarin masifar da suka shiga kafin a ceto su.

Kara karanta wannan

Borno: Mutanen Maiduguri sun wayi gari da labari mai daɗi bayan ambaliyar da ta afku

Mamakon ruwan sama da aka fara a daren Litinin ya lalata madatsar ruwa ta Alau, lamarin da ya jawo ambaliya da ta lalata gidaje, asibitoci da makarantu.

Ambaliya: Goni Ba Usman, wani magidanci da ke neman matarsa da 'ya'yansa da suka bace a Maiduguri.
Magidanci na neman matarsa da ƴaƴansa 5 bayan ambaliyar ruwa a Maiduguri. Hoto: @GovernorAUF
Asali: Twitter

Wadanda aka samu nasarar ceto su, sun godewa Allah amma sun ce iyalansu da dama sun makale a wuraren da ceton ya gaza zuwa gare su, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Iyalina sun bata a ambaliya" - Magidanci

An ga Goni Ba Usman, wanda ya tsira daga ambaliyar ya na kuka a gindin wata bishiya, ya na juyayin bacewar matarsa ​​da ‘ya ’yansa biyar.

Goni Ba Usman ya shaidawa wani ma'aikacin agajin gaggawa a sansanin da aka warewa wadanda aka ceto cewa:

"Na yi wa matata da 'ya'yana ganin karshe ne a ranar Talata da misalin karfe 6:30 na safe. Ka na ba ni ruwa, ta yaya zan iya sha alhali ban ga iyalina ba tun bayan ambaliyar?"

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa da aka wayi gari da su a Maiduguri bayan ambaliya

Duk da ziyarar da ya kai sansanin Babagana Wakil an ce Goni Ba Usman ya kasa samun iyalansa da suka bata.

"InnalilLahi Wa'inna ILaihi Rajiun (daga Allah muka zo kuma gareshi ne makomarmu)," Goni ya ci gaba da furtawa yayin da wasu ke lallashinsa.

"Na bar makwabta a wahala" - Tijjani

Wani da iftila'in ya ritsa da shi mai suna Abubakar Tijjani wanda sojoji suka ceto, ya bayyana cewa sun bar mutane cikin mawuyacin hali.

"Sama da mutane 50 da suka hada da maza, mata, da yara na baro sun samu mafaka a gidan da na koma. Adadin yana ci gaba da karuwa yayin da ake gudanar da ayyukan ceto."

- A cewar Malam Tijjani.

Tijjani ya lura cewa kayayyakin da ake amfani da su na ceton sun fara yin karanci sosai yayin da ake ci gaba da ceto mutane da yawa.

Fintiri ya kai tallafin N50m Borno

Kara karanta wannan

Ambaliya: Mutane sama da 200,000 sun rasa gidaje, yara sun bace a Maiduguri

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri ya ziyarci jihar Borno domin jajanta masu kan ambaliyar ruwan da ta mamaye Maiduguri.

Bayan ganin irin barnar da ambaliyar ta yi, Gwamna Fintiri ya ba Gwamna Babagana Umara Zulum tallafin N50m da kuma jiragen ruwa guda shida.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.