Ambaliyar Borno: Gwamna a Arewa Ya ba Zulum Tallafin N50m da Jirage 6
- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri da na Legas, Babajide Sanwo-Olu sun ziyarci Maiduguri domin duba ambaliya
- A yayin ziyarar ne Gwamna Fintiri ya ba gwamnan Borno Babagana Umara Zulum tallafin N50m da kuma jiragen ruwa shida
- Gwamnan Adamawa ya ce wannan lokaci ne na hada karfi da karfe domin ragewa mutanen da ambaliyar ta shafa radadin da suke ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya ba gwamnatin jihar Borno tallafin N50m da jiragen ruwa shida domin tallafawa al’ummomin da ambaliya ta shafa.
An sanar da bayar da tallafin ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya fitar a ranar Alhamis.
Gwamna Fintiri ya ba Zulum tallafin N50m
A yayin mika tallafin ga Gwamna Babagana Zulum, Gwamna Fintiri ya nuna bukatar hada karfi da karfe domin rage radadin al’ummar da ambaliyar ruwa ta shafa, inji Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fintiri ya nuna matukar kaduwarsa kan asarar rayuka da lalacewar gidaje da dukiyoyin jama'ar Maiduguri sakamakon ambaliyar.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar matakai na magance matsalar ambaliyar ruwa a fadin kasar nan.
Gwamnoni sun kai ziyara Borno
Domin nuna damuwarsu kan abin da ya faru a Maiduguri, Gwamna fintiri tare da gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu sun zagaya tare da Gwamna Zulum inda ambaliyar ta shafa.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Gwamna Fintiri ya bayyana cewa:
"A yau (Alhamis) na ziyarci Maiduguri domin kasacewa tare da 'yan uwanmu maza da mata da ambaliyar ruwa ta shafa. Na yi matukar kaduwa da abin da idanuwana suka gani.
"Jihar Adamawa na tare da Borno a wannan mawuyacin hali. Mun samar da tallafin kayayyaki da kudi ga Babagana Zulum domin ayyukan ceto."
Abin da ya jawo ambaliyar Maiduguri
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar raya shiyyar Arewa maso Gabas (NEDC) ta ce rashin karkon gini da cushewar ruwa a madatsar Alau ya jawo ambaliya a Maiduguri.
Babban daraktan gudanarwa da harkar kudi na hukumar NEDC, Garba Iliya ya ce a halin yanzu an ba da kwangilar gyara madatsar ruwan domin kare faruwar hakan a gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng