Badakalar N440m: ICPC Ta Dura kan Kakakin Majalisar Kano da Wasu Mutane 4

Badakalar N440m: ICPC Ta Dura kan Kakakin Majalisar Kano da Wasu Mutane 4

  • Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta gayyaci jagororin majalisar dokokin jihar Kano domin bincike
  • Kakakin majalisar, mataimakin kakaki, shugaban masu rinjaye da magatakarda ne hukumar ta gayyata domin su amsa wasu tambayoyi
  • ICPC ta ce ta gayyace su bisa zargin su na da hannu a badakalar kwangilar sayo magunguna ta N440m na kananan hukumomin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Hukumar ICPC ta gayyaci kakakin majalisar Kano Jibril Falgore, mataimakin kakakin majalisar, Muhammad Butu da wasu mutane uku domin amsa tambayoyi.

An rahoto cewa gayyatar dai wani bangare ne na binciken badakalar kwangilar magunguna ta Naira miliyan 440 a kananan hukumomi 44 na jihar.

Kara karanta wannan

NNPP ta fito da mace a matsayin 'yar takarar shugaban karamar hukumar Kano

Hukumar ICPC ta gayyaci kakakin majalisar Kano da wasu mutane 4 kan badakalar kwangila
Badakalar kwangila: Kakakin majalisar Kano da mutane 4 za su gurfana gaban ICPC. Hoto: Jibril Ismail Falgore, ICPC Nigeria
Asali: Facebook

Hukumar ICPC za ta waiwayi majalisar Kano

A ranar Alhamis ne hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta aike masu da takardar gayyatar, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran wadanda aka gayyata su ne: Shugaban masu rinjaye Lawan Dala; Magatakardar majalisar, Bashir Diso da babban sakatare na ma'aikatar kananan hukumomi.

Baya ga babban sakataren da zai gurfana gaban jami'an ICPC a ranar 18 ga Satumba, hukumar ta shirya titsiye kakakin majalisar da sauran 'yan majalisar a ranar 19 ga Satumba.

ICPC na binciken badakalar kwangila a Kano

Wasikar gayyatar mai kwanan watan 12 ga Satumba da aka aikewa da wadanda aka gayyata, ta bayyana cewa:

“Hukumar na binciken zargin karya dokar da suka shafi cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka masu alaka, mai lamba 5 2000.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bankado ma'aikatan lafiya da ke tafka mata sata, ta dauki mataki

“Bisa ga sashe na 28 na dokar, za ka bayyana domin amsa tambayoyi a gaban wadanda aka bayyana sunayensu a kasa a hedkwatar ICPC, Abuja.
"Ana sa ran za ka zo da ko dai lauya, jami'in kotu na zaman lafiya (JP), ma'aikacin cibiyar ba da taimakon shari'a (LIC), ko kuma kowane mutum da ka zaɓa."

Kano: PCACC na binciken kwangilar magani

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta samu umarni rufe wani asusun banki mai dauke da N160m.

Wannan dai na daga cikin nasarorin da hukumar ta samu a yayin da ta ke binciken badakalar kwangilar magungunta ta N440m da aka ba kamfanin NOVOMED ba bisa ka'ida ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.