Zamfara: Sabon Rikici Ya Barke Tsakanin APC da Gwamnatin PDP kan Matsalar Tsaro

Zamfara: Sabon Rikici Ya Barke Tsakanin APC da Gwamnatin PDP kan Matsalar Tsaro

  • Sabuwar rigima ta sake barkewa tsakanin jam'iyyar APC da gwamnatin PDP mai mulki a Zamfara kan matsalar tsaron da ta addabi jihar
  • Jam'iyyar APC ta zargi gwamnatin Dauda Lawal da gaza cika alkawarin kawo karshen matsalolin tsaro bayan shekara daya a mulki
  • Sai dai gwamnatin Dauda ta yi wa APC martani kan halin da jihar ta ke ciki, inda ta ce gwara mulkinta kan na gwamnatin Bello Matawalle

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Jam’iyyar APC reshen Zamfara ta gargadi Gwamna Dauda Lawal da ya daina dora wa magabacinsa Bello Mattawalle da APC alhakin tabarbarewar tsaro a jihar.

A wata sanarwa daga kakakin jam'iyyar, Alhaji Yusuf Idris, APC ta ce har yanzu Gwamna Dauda bai magance matsalar tsaro a jihar ba kamar yadda ya yi alkawari.

Kara karanta wannan

Yunwa: Wasu Gwamnonin jihohin Kudu sun fitar da tsarin wadata jama'a da abinci

APC ta zargi gwamnatin Dauda Lawal da gaza shawo kan matsalar tsaro a Zamfara
An fara cacar baki tsakanin APC da gwamnatin PDP kan matsalar tsaro a Zamfara. Hoto: @daudalawal_, @Bellomatawalle1
Asali: Twitter

APC ta zargi gwamnan da dora alhakin gazawar gwamnatinsa ga magabacinsa Matawalle maimakon yaki da rashin tsaro a jihar, inji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar APC ta caccaki Dauda da PDP

Alhaji Yusuf ya ce Gwamna Dauda ya ci gaba da zargin gwamnatin APC da ta shude a jihar alhalin ita (gwamnatin PDP) ta gaza cika alkawurran da ta yi wa jama’a.

“Dauda ya yi amfani da rashin tsaro ya bata gwamnatin Matawalle, ya yi alkawarin kawar da kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta a cikin watannin farko na mulkinsa.
“Sai dai, bayan ta kasa shawo kan matsalolin tsaron, gwamnatin Dauda ta sake juyowa kan APC, ta na mai cewa ita ce dalilin da ya sa PDP ba za ta iya kawar da ‘yan bindigar ba.”

- A cewar Alhaji Yusuf.

Gwamnatin PDP ta yi wa APC martani

Kara karanta wannan

Zaben Edo: APC ta fasa sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

A wani martani da gwamnatin Zamfara ta yi wa APC, ta kare gwamnatin Dauda kan zarginta da ware sama da Naira biliyan 1 domin yin sulhu da 'yan bindiga.

Sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Nakwada, ya shaida cewa takardun da ake yadawa na biyan kudin na bogi ne, an kirkire su ne domin a yaudari jama'a da bata sunan gwamnati.

Shi ma da yake karyata ikirarin APC na cewa Gwamna Lawal bai tabuka komai ba kan yaki da tsaro a shekararsa ta farko, Mustafa Jafaru Kaura, ya ce ‘yan APC na soki burutsu ne kawai.

Mustafa Jafaru Kaura wanda mai tallafawa Gwamna Dauda ne na musamman ya ce:

“Gwamna Lawal ya taka rawar gani wajen yaki da ‘yan bindiga a jihar idan aka kwatanta da tsohuwar gwamnatin Bello Mattawalle."

Tsaro: Turji ya kalubalanci Matawalle

A wani labarin, mun ruwaito cewa hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Bello Turji ya zargi tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da goyon bayan ayyukan ta'addanci.

Kara karanta wannan

Wani Malamin Addini ya daɓawa matarsa wuƙa har lahira, gwamna ya ɗauki mataki

A wani faifan bidiyo da ya fitar, Bello Turji ya yi ikirarin cewa ya na da hujjoji da zai kare zargin da ya yi na cewa gwamnatin da ta shude a Zamfara ce ta daurewa ta'addanci gindi a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.