'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an Sojoji a Wani Farmaki a Jihar Arewa

'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an Sojoji a Wani Farmaki a Jihar Arewa

  • Ƴan bindiga sun kai hare-hare a kan titin hanyar Gusau zuwa Funtua da safiyar ranar Alhamis, 12 ga watan Satumban 2024
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutum bakwai ciki har da sojoji guda uku masu yi wa injiniyoyi ƴan ƙasashen waje rakiya
  • Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga, Dan Yusuf ne ya kai hare-haren guda biyu a babban titin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga sun kai hari kan ma'aikatan kamfanin gine-gine a hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan a yayin harin sun kashe mutane bakwai ciki har da sojoji uku waɗanda suke yi wa injiniyoyi ƴan ƙasashen waje rakiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare babbar hanya a Arewa, sun sace matafiya masu yawa

'Yan bindiga sun hallaka sojoji a Zamfara
'Yan bindiga sun hallaka sojoji uku a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan bindiga sun kai hare-hare a Zamfara

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a Yandoton-Tsafe, cikin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, da misalin ƙarfe 9:00 na safe, a ranar Alhamis.

Harin shi ne na biyu da ƴan bindiga suka kai kan hanyar Gusau zuwa Funtua cikin ƴan awanni sa’o’i kaɗan.

Harin na farko ya faru ne a ƙauyen Kucheri da ke cikin ƙaramar hukumar Tsafe yayin da wasu gungun ƴan bindiga suka tare babbar hanyar Funtua zuwa Gusau tare da yin awon gaba da matafiya da dama.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa hare-haren guda biyu, ana kyautata zaton ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga, Dan Yusuf, wanda ƙani ne Ado Aliero, ya kai su.

Ƴan bindiga sun hallaka sojoji

Kara karanta wannan

Sojoji sun kutsa cikin daji, sun hallaka ƴan bindigar da suka addabi mutane a Arewa

Har ila yau, wani mazaunin garin Tsafe, Ibrahim Umar, ya ce an kai harin na biyu ne kan wasu ma’aikatan kamfanin gine-gine a Ƴandoton Tsafe, inda suka kashe kimanin mutane bakwai ciki har da sojoji uku.

Ya ce ƴan bindigar sun farmaki wurin da ake aikin ne a kan babura, suka buɗe wuta kan ma’aikatan da ba su ji ba, ba su gani ba.

"Sojojin da ke kare ma’aikatan sun daƙile harin, amma an kashe kusan mutane bakwai ciki har da sojoji a yayin arangamar."
"An kuma ce ƴan bindigan sun yi garkuwa da wani injiniya ɗan kasar waje a yayin harin."

- Ibrahim Umar

Ƴan bindiga sun kai hare-hare

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kashe mutane biyar tare da yin garkuwa da wasu da dama a Kaduna da ke yankin Arewa maso Yamma.

Ƴan bindigan sun kai harin ne kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a ƙauyen Kallah Afogo a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng