'Yan Kasuwar Fetur Sun Harzuka Shi, Gwamna Ya Kara Barazana, Ya Rufe Gidajen Mai

'Yan Kasuwar Fetur Sun Harzuka Shi, Gwamna Ya Kara Barazana, Ya Rufe Gidajen Mai

  • Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru ya fusata kan yadda wasu gidajen mai ke yin algus wajen sayar wa jama'a man fetur
  • Francis Nwifuru ya rufe wasu gidajen mai da aka kama da aikata laifuffuka, inda ya yi barazanar daukar wasu matakan
  • Ya ce idan ba su zama masu gaskiya da amana ba, gwamnatinsa ba za ta gajiya wajen daukar matakai a kansu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ebonyi - Gwamnatin Ebonyi ta kama wasu gidajen mai guda uku a babban birnin jihar, Abakaliki da yi wa jama'a algus, duk da tsadar da fetur ya yi.

Gwamnan jihar, Francis Nwifuru ya bayyana cewa ba za su saurara wa duk wadanda aka kama da kara jefa jama'a a cikin kuncin rayuwa ba.

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur ya tilastawa Gwamna karawa ma'aikata hutu a kowane mako

Francis
Gwamna ya rufe gidajen mai a Ebonyi Hoto: Francis Nwifuru
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa gwamnan ya kama wasu gidajen mai da ake zargi su na musguna wa mazauna jihar.

Matakan gwamnan Ebonyi na hana tsadar fetur

Sanarwar da mataimakin gwamnan Ebonyi na musamman a bangaren fetur, Nwafor Nnaemeka ya fitar, ta ce an rufe wasu gidan mai uku a Abakaliki.

Daga cikin laifuffukan da aka kama su da aikata wa akwai rage litar mai, kara farashin fetur ba isa ka'ida ba da sauran abubuwan da su ka saba doka.

Gwamnan Ebonyi ya yi gargadi kan man fetur

Gwamna Francis Nwifuru ya ce gwamnatinsa ba za ta saurara wa duk masu gidajen mai da aka kama su na tsawwala wa jama'a ba.

Gwamnan ya yi barazanar kara rufe wasu gidajen mai a dukkanin fadin jihar matukar aka samu labari da tabbatar da cewa su na aikata ba dai-dai ba.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Rundunar sojoji ta mika ta'azziyya Borno, za a taimaka wa jama'a

Tsadar fetur: Gwamnan Ebonyi zai kara albashi

A baya mun ruwaito cewa gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya amince da kara wa ma'aikatan gwamnatin jiharsa albashi a lokacin da ake kuka da karuwar farashin fetur.

Gwamna Nwifuru ya kara da cewa duk da ba wai ya na nufin za a biya kowane ma'aikaci N70,000 ba ne, amma gwamnatinsa na da shirin inganta rayuwar ma'aikata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.