Mawakin Musulunci Ya Fadi Dalilin Yin Murabus daga Matsayin Hadimin Gwamna
- Mutane da dama sun sha mamaki bayan murabus din hadimi na musamman ga Gwamna AbdulRahman AbdulRazak
- Alhaji Alhaji Ibrahim Labeeka wanda mawakin yabo ne ya ajiye aikinsa a yau Laraba 12 ga watan Satumbar 2024
- Labeeka a cikin wata sanarwa ya koka kan yadda yake karbar albashi ba tare da cimma abin da ake bukata ba a ofis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kwara - Hadimin Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na jihar Kwara a bangaren nishadi da wakoki ya yi murabus daga mukaminsa.
Alhaji Ibrahim Labeeka ya ajiye aikinsa ne saboda abin da ya kira rashin sanin ainihin abin da ya ke yi.
Kwara: Hadimin gwamna ya yi murabus
Labeeka ya ajiye aikin ne a cikin wata sanarwa da Legit Hausa ta samu a yau Alhamis 12 ga watan Satumbar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sahara Reporters ta ruwaito cewa mawakin Musulunci ya koka kan yadda yake karbar albashi ba tare da cimma abin da ake bukata ba ya saba ka'ida.
Mawakin ya ce rashin sanin takamaiman aikinsa da suka fi karfinsa na daga dalilin rashin cika ka'idar aiki da ya ke yi, cewar rahoton Punch.
Akalla hadimin ya shafe shekara daya da kuma watanni bakwai yana rike da mukamin a jihar.
Daga bisani, mawakin ya ya godewa gwamnan kan damar da ya ba shi domin ba da tashi gudunmawa a jihar.
Labeeka ya roki alfarma a wurin gwamna
Har ila yau, a cikin sanarwar da ya fitar, Labeeka ya bukaci a tsayar da albashinsa nan take.
Wannan mataki ya ba mutane mamaki matuka ganin cewa Labeeka na daya daga cikin masu kokari a gwamnatin Kwara.
Duk da bai bayyana ƙarara dalilin yin murabus din ba, amma a bayyane ya nuna rashin sanin ainihin aikinsa ya hana shi samun damar cimma abin da ake bukata a gare shi.
Tsadar mai: Gwamnatin Kwara ta tausayawa al'umma
Kun ji cewa ana cikin mawuyacin hali bayan kara farashin mai a Najeriya, Gwamnatin jihar Kwara ta agazawa al'ummarta.
Gwamnatin ta ba da umarnin samar da bas musamman a cikin birni domin zirga-zirgar jama'a wurare daban-daban.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng