'Bello Turji Na Kokarin Sauya Suna': Bulama Ya Fallasa Shirin Hatsabibin Dan Bindiga

'Bello Turji Na Kokarin Sauya Suna': Bulama Ya Fallasa Shirin Hatsabibin Dan Bindiga

  • Bulama Bukarti ya bayyana cewa Bello Turji na kokarin wanke kansa tare da sauya sunansa daga 'dan ta'adda' zuwa mai kare Fulani
  • A wata tattaunawa da aka yi da fitaccen lauyan, ya ce Bello Turji ba kowa ba ne face matsoraci da ke farautar fararen hula marasa karfi
  • A yayin da ya bayyana dalilai uku da suka sa Bello Turji ke yawan sakin bidiyoyi a kwanan nan, Bulama ya ce akwai laifin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fitaccen lauyan Najeriya, Bulama Bukarti ya yi martani mai zafi ga dan ta'addan daji Bello Turji bayan ya yi barazana ga masu magana kan ta'adinsa.

Bulama Bukarti ya ce Bello Turji ya dage da sakin bidiyo a kwana kwanan nan saboda wasu dalilai uku wadanda ya ce dan ta'addan ba zai cimma ko daya ba.

Kara karanta wannan

"Na yi da Shekau ma": Bulama Bukarti ya yi martani bayan Bello Turji ya gargade shi

Bulama Bukarti ya yi magana kan dalilin da ya sa Bello Turji ke sakin bidiyo a kai a kai
Bulama Bukarti ya zargi Bello Turji da kokarin sauya sunansa daga Dan bindiga zuwa mai kare Fulani. Hoto: Audu Bulama Bukarti.
Asali: Facebook

A wata tattaunawa da aka yi da Bukarti da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, ya bayyana cewa Bello Turji matsoraci ne mai farmakar farar hula.

Bulama Bukarti ya bayyana dalilai uku da suka sa Bello Turji ke yawan fitowa yana magana a bidiyo a kwanan nan:

1. "Bello Turji ya na ikirarin kare Fulani"

Lauyan ya ce Bello Turji na kokarin wanke kansa daga matsayin dan ta'adda, da kuma kokarin nuna kansa a matsayin mai kare al'ummar Fulani.

Bulama ya ce:

"Amma wannan kokarin nasa ba zai yi nasara ba, domin tuni duniya ta yi masa tambari da: hatsabibin mai garkuwa da mutane, dan fashi da makami da kuma makashi."

Al’ummar Fulani na jin haushin sa saboda sun gano cewa shi dan ta'adda ne wanda ke bata musu suna, a cewar lauyan.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya yi sabon bidiyo, ya tura sako ga Pantami, Dan Bello da malamin Musulunci

2. "Turji Ya na kokarin razana mu"

Bulama Bukarti ya yi ikirarin cewa yawan maganganun da Bello Turji ke yi a 'yan kwanakin nan wata hanya ce ta tsorata masu sukar ayyukansa da neman kawar da shi.

"Sai dai ƙoƙarinsa na tsoratar da ni ba zai yi tasiri ba. Shi ba komai ba ne face matsoraci da ke farautar fararen hula sannan kuma ya rika buya kamar wani bera."

- A cewar Bulama.

Lauyan ya ce idan har Bello Turji na tunanin shi wani jarumi ne, to ya fito ya yi gaba da gaba da jami'an soji.

3. "Gwamnati ta gaza yin maganin Turji"

Fitaccen lauyan ya ce Turji ya na jin kwarin gwiwar yin wadannan bidiyoyi tare da yin barazana ne saboda gwamnati ta gaza yin maganinsa yadda ya kamata.

"An ba shi damar kashewa, raunatawa, yin fashi, fyade da bautar da jama'a ba tare da wani hukunci ba, wanda hakan ya kara masa izza da kuma kariya daga shari'a."

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu: Malami ya hango shekarar da tsadar rayuwa za ta kare a Najeriya

- Inji Bulama.

Duba bidiyon a kasa:

Bello Turji ya saki sabon bidiyo

A wani labarin, mun ruwaito cewa hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Bello Turji gargadi fitaccen lauya da ake kira Bulama Bukarti kan fitar da wasu takardun haraji na garin Moriki.

A cikin wani faifan bidiyo na dan ta'addan da aka fitar ranar 11 ga Satumba, Turji ya ce takardun da Bulama ya fitar gaskiya ne amma akwai kura kurai a bayanan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.