Tsadar Abinci: Gwamna Ya Dauki Manyan Matakai 2, Ya Ja Kunnen Yan Kasuwa

Tsadar Abinci: Gwamna Ya Dauki Manyan Matakai 2, Ya Ja Kunnen Yan Kasuwa

  • Gwamnatin Ogun ta bayyana takaicin yadda ake samun hauhawar farashin abinci a kasuwannin jihar
  • Dapo Abiodun ya ce gwamnatinsa za ta dauki kwararan matakai da za su dakile hauhawar farashi abinci
  • Gwamnatin ta gargadi ga yan kasuwar jihar da ake zargi da tsula farashin kayan abinci su wahalar da jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar OgunGwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin daukar matakan saukaka tsadar abinci.

Gwamna Abiodun ya ce ana shirye-shiryen bijiro da kayyade farashin kayayyaki a kasuwannin jihar domin sa wa yan kasuwa linzami, musamman ta fuskar karin kudin kayan masarufi.

Kara karanta wannan

Kwanaki da alakantasa da 'yan bindiga, gwamna a Arewa ya tattago aikin kasuwar N3.6bn

Jihar Ogun
Gwaman Ogun zai kayyade farashin kaya a kasuwanni Hoto: Hoto: @DapoAbiodunCON
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa haka kuma gwanma Dapo Abiodun ya kara da cewa akwai kyautata zaton matakan gwamnati zai saukaka hauhawar farashin da ake samu a kasuwanni.

Gwamnan Ogun ya dira kan yan kasuwa

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa gwamna Dapo Abiodun ya dakatar da karbar haraji kowane iri a kasuwannin jihar Ogun domin kawo sauki ga jama'a.

Amma gwamnan ya ce za a ci gaba da karbar harajin bunkasa kasuwanni saboda amfaninsu wajen ci gaban kasuwannin jihar.

Dalilin daukar matakan gwamnatin Ogun

Gwamnatin jihar Ogun ta ce sababbin matakan da ta dauka ya biyo bayan kokarinta na dakile matsalar abinci wanda hauhawar farashin abinci ke sabbabawa a jihar.

Ya ce daga yanzu, ba a amince wasu kungiyoyin kasuwa ko jama’a su rika tilastawa jama’a biyan haraji a kasuwanni a fadin jihar ba.

Kara karanta wannan

"Zaluncin gwamnatin Tinubu ya fi na soja:" Atiku ya soki yadda ake murkushe kungiyoyi

Gwamnatin Ogun ta karbi bukatun matasa

A baya kun ji labarin cewa matasan da ke shirin zanga-zangar matsin rayuwa sun bukaci gwamna Dapo Abiodun ya tabbatar ya samar da jami'an da za su tsare su.

Matasan sun mika bukatar motocin bas bas da za su yi jigilar su yayin da su ke shirin zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ke jawo yunwa a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.