Hukumar CCB Ta Bayyana Abubuwa 2 da Ke Kawo Cikas a Yaki da Rashawa a Najeriya

Hukumar CCB Ta Bayyana Abubuwa 2 da Ke Kawo Cikas a Yaki da Rashawa a Najeriya

  • Hukumar kula da da'ar ma'aikata ta ce karancin kudi da kuma rashin isassun ma’aikata ne suka kawo cikas ga yaki da rashawa a
  • Shugaban CCB, Barista Murtala Kankia ya bayyana cewa kasafin N173m da ake warewa hukumar a halin yanzu ba ya wadatar da su
  • Barista Kankia ya bayyana haka ne a yayin bikin kaddamar da sashen kwato kayan sata daga barayin kasa tare da alkintasu a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi magana kan namijin kokarin da ta ke yi na kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar nan da kuma abubuwan da ke kawo mata cikas.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bankado ma'aikatan lafiya da ke tafka mata sata, ta dauki mataki

Ta bakin hukumar kula da da'ar ma'aikata (CCB), gwamnatin ta ce abubuwa biyu ne suka zamo ja gayya a kawo cikas ga shirinta na samar da kasa marar rashawa.

Hukumar CCB ta yi magana kan abubuwan da ke kawo cikas ga yaki da cin hanci da rashawa
Gwamnati ta ce karancin kudi da rashin wadatattun ma'aikata ne kawo cikas ga yaki da rashawa. Hoto: @CCBNigeria
Asali: Twitter

Cikas a yaki da rashawa a Najeriya

Mukaddashin shugaban CCB, Barista Murtala Kankia ya bayyana cewa rashin wadataccen kasafi dakarancin ma'aikata ne ke gurgunta yaki da rashawa, inji rahoton Daily Trust.

Barista Murtala ya bayyana haka ne a yayin bikin kaddamar da sashen kwato kayan sata daga barayin kasa tare da alkintasu a ranar Laraba a Abuja.

“Daya daga cikin manyan kalubalen da muke fuskanta a yaki da cin hanci da rashawa shi ne rashin isassun kudi da ma’aikata."

- A cewar Barista Murtala Kankia

Matsaloli a ayyukan hukumar CCB

Dangane da ayyukan hukumar kula da da'ar ma'aikata, Premium Times ta ruwaito Barista Murtala ya sanar da cewa:

Kara karanta wannan

'Yan sanda 39 a kauyuka 200," Gwamna Radda ya fayyace matsalar tsaron Katsina

"Mu ne ke da alhakin kula da batun bayyana kadarorin ma'aikata a dukkanin ma’aikatun gwamnati, ciki har da na jihohi 36 da kananan hukumomi 774.
"Kasafin kudin da ake ware mana a halin yanzu ya yi kadan. Ba ya wuce N173m, wanda ko kusa ba ya wadatar da mu a gudanar da sahihin tantance kadarorin ma'aikata."

Ya kuma ce ma’aikatan CCB sun ragu sosai a tsawon shekarun nan, abin da ya kara jawo tabarbarewar ayyukansa.

Tinubu ya nada shugaban CCB

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Dakta Abdullahi Usman Bello a matsayin shugaban hukumar da’ar ma’aikata (CCB).

Dakta Bello kwararre ne wanda ya shafe sama da shekaru 25 yana aikin ba da shawarwari, harkar banki, tabbatar da doka, ayyukan kudi da dai sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.