Bayan Shafe Kwanaki a Hannun 'Yan Bindiga, Jagoran PDP ya Shaki Iskar 'Yanci

Bayan Shafe Kwanaki a Hannun 'Yan Bindiga, Jagoran PDP ya Shaki Iskar 'Yanci

  • Rundunar yan sandan jihar Oyo ta tabbatar da ceto jagoran jam'iyyar PDP, Benedick Akika da yan ta'adda su ka sace
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Adéwálé Osifeso ne ya tabbatar da haka, ya ce tun bayan da aka sace shi suka shiga aiki
  • 'Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun farmaki gidan Cif Benedick Akika, da ke karamar hukumar Lagelu a jihar Oyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Oyo - Rundunar 'yan sandan Oyo ta bayyana cewa an yi nasarar ceto jigo a jam'iyyar PDP, Benedick Akika wanda aka sace a gidansa da ke karamar hukumar Lagelu a jihar.

Kara karanta wannan

"Za mu hargitsa komai": NLC ta yi barazana kan zaben dan takarar gwamnan PDP a bidiyo

Jami'in hulda da jama'a na rundunar a jihar Oyo, Adéwálé Osifeso ya tabbatar da cewa an yi nasarar ceto Cif Akika a ranar Laraba.

Police
Yan sanda sun ceto jagoran PDP daga hannun yan bindiga Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a ranar 4 Satumba, 2024 ne yan bindiga dauke da miyagun makamai suka kutsa gida jigon PDP da ke Idi Ape, Olorunda-Aba a jihar Oyo.

Yadda yan sanda su ka ceto jigon PDP

Rundunar 'yan sandan Oyo ta bayyana cewa tun bayan sace jagora a PDP ne jami'anta su ka shiga farautar yan bindigar da su ka yi satar.

Nigerian Tribune ta wallafa cewa yan sanda sun shiga neman inda aka boye Cif Akika a yankunan jagun, Ijebu Ode in jihar Ogun, Ore, jihar Ondo da Uselu a jihar Edo.

Halin da jagoran PDP yake ciki

Kara karanta wannan

Bayan ambaliya a Borno da Bauchi, an shiga fargaba a garuruwan Yobe

Kakakin yan sandan Oyo, Adéwálé Osifeso ya bayyana cewa yanzu haka Cif Akika ya na asibiti inda ake duba lafiyarsa.

Ya ce da zarar an kammala duba halin da ya ke ciki za a sada shi da yan uwansa domin bayan shafe kwanaki takwas bai gansu ba.

'Yan bindiga sun sace jigon PDP

A wani labarin kun ji yadda yan bindiga su ka kutsa gidan jigon PDP, Benedick Akika a jihar Oyo inda su ka fara barazanar harbe iyalansa idan su ka yi kokarin yin gardama.

Daga baya yan bindigar da suka aikata danyen aikin sun sace Cif Akika tare da awon gaba da shi zuwa inda ba a sani ba, sannan ba su bayyana wa iyalansa maganar fansa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.