Ana Kukan Karancin Makaman 'Yan Sanda, An Kama Harsashi Za a Mikawa 'Yan Bindiga

Ana Kukan Karancin Makaman 'Yan Sanda, An Kama Harsashi Za a Mikawa 'Yan Bindiga

  • Asirin wani mai sayen makami da kayan fada ga yan bindiga masu garkuwa da mutane ya tonu a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya
  • Yan sa kai a jihar Katsina sun kama tulin harsashi yayin da mugun mutumin ya ɓoye su a cikin wata motar haya da yake tafiya Batsari
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa mutumin da ke dauke da kayan fadan ya sulale yayin da yan sa kai suka tare motar suna binciken kwaƙof

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Yan sa-kai a jihar Katsina na cigaba da ƙoƙari domin kawo karshen yan bindiga masu garkuwa da mutane.

A ranar Laraba ne masu aikin sa-kai a suka tare wata mota suna bincike inda suka kama tulin harsashi.

Kara karanta wannan

Borno: Mutanen Maiduguri sun wayi gari da labari mai daɗi bayan ambaliyar da ta afku

Dikko Radda
An kama harsashi a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Jami'in yada labaran gwamnatin Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammad ne ya wallafa yadda abin ya faru a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama kayan harsashi a jihar Katsina

Yan sa kai sun tabbatar da cewa sun kama tarin harsashi da ake zargin ana ƙoƙarin miƙa shi ga yan bindiga ne domin yakar al'umma.

Bayanai sun nuna cewa harsashin da yan sa kai suka kama na bindiga ƙirar AK-47 ne da bindiga ƙirar GPMG.

Yadda aka kama harsashi a Katsina

An ruwaito cewa wani mutum ne ya dauko harsashin a motar haya da ta dauko mutane 17, maza hudu da mata 13.

A yayin da yan sa kai suka tare motar suna bincike a hanyar Batsari sai suka ga an boye tulin harsashi a kasan sirdin motar.

Wanda ya dauko harsashin ya gudu

Yan sa-kai su tabbatar da cewa mutumin da ya dauko harsashin da ake zargin zai mika ga yan bindiga ne ya sulale yayin da ake binciken motar.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa da aka wayi gari da su a Maiduguri bayan ambaliya

An ruwaito cewa tun ana tafiya mutumin ya nuna alamar kamar ba shi da gaskiya kuma ya nemi ya zauna a baya yayin shiga motar.

Gwamna zai ba mutan bindiga a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya nuna takaici kan yadda yan bindiga ke kashe mutane da sace su a Arewacin Najeriya.

Dikko Umaru Radda ya ce a shirye yake ya ba mutane bindigogi domin su rika fafatawa da yan ta'adda masu garkuwa da mutane a Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng