Bello Turji: IPOB Ta Gargadi Tsohon Hadimin Buhari, Ta Fadi Laifin Nnamdi Kanu
- Kungiyar da ke rajin kafa kasar Biafra, IPOB ta yi magana kan hada Nnamdi Kanu da rikakken dan ta'adda, Bello Turji
- Kungiyar ta gargadi Bashir Ahmad bayan ya kwatanta Turji da Nnamdi Kanu kan ta'addanci a Najeriya
- IPOB ta ce Kanu dan Biafra ne wanda ke neman kafa kasar ta hanya mai kyau yayin da Turji ke ta'addanci karara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Enugu - Kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ta gargadi Bashir Ahmad game da kalamansa.
Kungiyar ta ja kunnen tsohon hadimin Muhammadu Buhari da ya guji kwatanta Bello Turji da Nnamdi Kanu.
Bello Turji: IPOB ta gargadi Bashir Ahmad
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar, Emma Powerful ya fitar wanda Punch ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Powerful ya ce Kanu kwata-kwata bai goyon bayan ta'addanci kamar yadda Turji da yan uwansa ke yi, Daily Post ta ruwaito wannan.
Ya ce laifin da Kanu ya yi wa shugabannin Fulani kawai guda daya ne domin ya kafa dakarun tsaron yankin Kudu maso gabas.
Har ila yau, Powerful ya bukaci Bashir Ahmad ya cire sunan Kanu a ta'addancin da suka kawo Arewacin Najeriya.
IPOB ta fadi laifin Nnamdi Kanu
"IPOB ta na gargadin Bashir Ahmad ya bar hada Nnamdi Kanu da ba shi da bindiga da dan uwansa dan ta'adda, Bello Turji."
"Kanu dan Biyafara ne na gaskiya bai yadda da ta'addanci ba, laifin kawai da ya yi wa masu goyon bayan ta'addanci irinsu Bashir shi ne kirkirar jami'an tsaron ESN saboda kalubalantar Fulani."
"Manyan Fulani suna ganin Kanu a matsayin barazana a shirinsu game da Najeriya shiyasa suke amfani da sojoji domin cin zarafinsa."
- Emma Powerful
Hajiya Dada: Bashir Ahmad ya kare Buhari
Kun ji cewa wasu mutane sun yi ta ce-ce-ku-ce a kafofin sadarwa kan rashin halartar tsohon shugaba Muhammadu Buhari jana'izar Dada.
Sai dai tsohon hadiminsa, Bashir Ahmad ya bayyana musababbin rashin halartar mai gidan nasa jana'izar da aka yi a Katsina.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban kasa, marigayi Umaru Musa Yar'Adua a asibitin jihar Katsina.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng