Kungiyar ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki, Ta Bayyana Dalilai
- Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) a jami'ar jihar Gombe ta tsunduma yajin aiki sakamakon rashin biya mata bukatu
- Shugaban ASUU na jami'ar jihar Gombe, Dakta Salihu Sulaiman Jauro ya bayyana abubuwan da gwamnati ta gaza yi musu
- Legit ta tattauna da wata daliba a jami'ar jihar Gombe, Zainab Abubakar domin jin halin da suka shiga bayan fara yajin aikin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Kungiyar malaman jami'a ta kasa reshen jami'ar jihar Gombe ta sanar da fara yajin aiki.
A yammacin yau Laraba ne kungiyar ta shiga yajin aikin bayan gwamnatin Gombe ta gaza biya mata bukatu.
Sanarwar da shugaban ASUU a jami'ar jihar Gombe, Dakta Salihu Sulaiman Jauro ya mikawa Legit ta nuna cewa sun shiga yajin aikin ne domin kare muradun jami'ar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki
Kungiyar ASUU a jami'ar jihar Gombe ta fara yajin aikin sai-baba-ta-gani daga yau Laraba, 11 ga watan Satumba.
Shugaban ASUU a jami'ar jihar Gombe, Dakta Salihu Sulaiman Jauro ya ce sun dauki matakin ne ba domin suna so ba sai dai kawai ya zama dole ne.
Dalilin shigan ASUU yajin aiki a Gombe
Kungiyar ASUU a jihar Gombe ta bayyana cewa a shekarar 2021 ta shiga alkawari da gwamnati kan karin kudin gudanar da jami'ar amma abin ya gagara.
ASUU ta ce sun yi alkawarin ware N10m duk wata domin samun karin kudin gudanar da jami'ar amma sau biyu kawai gwamnatin ta cika alkawarin.
Daily Trust ta wallafa cewa hakan ya saka hukumar makarantar ƙirƙiro hanyoyin neman kudi a wajen dalibai domin sayen abubuwan amfani a jami'ar.
Maganar ƙarin albashin malamai
Kungiyar malaman ta ce tun da aka yi karin mafi ƙarancin albashi zuwa N30,000 gwamnatin Gombe ba ta saka su a cikin karin albashin ba.
Haka zalika kungiyar ta ce tsawon shekaru huɗu da suka wuce gwamnatin ba ta biya malaman da aka karawa matsayi bashin kudinsu ba.
Legit ta tattauna da dalibar jami'ia
Wata daliba a jami'ar jihar Gombe, Zainab Abubakar ta zantawa Legit cewa duk da a halin yanzu suna hutu amma yajin aikin zai kawo musu tsaiko.
Zainab Abubakar ta ce sun gama jarrabawa kuma malaman ba lallai su cigaba da duba takardun jarrabawar ba wanda hakan zai kawo jinkiri a harkar makarantar.
Dalibar ta yi kira ga gwamnatin jihar Gombe kan daukar matakin kawo karshen yajin aikin kafin hutunsu ya kare.
Gwamnan Gombe ya yiwa ASUU alkawari
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna ya yiwa malaman jami'ar Gombe alƙawarin biyan alawus-alawus ɗin da suka biyo bashi domin ka da su shiga yajin aiki.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce gwamnatinsa za ta fitar da N947,669,909.13 domin biyan alawus din a taron majalisar zartaswa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng