Bayan Ambaliya a Borno da Bauchi, An Shiga Fargaba a Garuruwan Yobe

Bayan Ambaliya a Borno da Bauchi, An Shiga Fargaba a Garuruwan Yobe

  • Gwamnatin Yobe ta shawarci mazauna kananan hukumomi tara su gaggauta daukar matakai yayin da ake sa ran ambaliya
  • Hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar ce ta bayar da gargadin, inda ta ce za a samu ambaliya ne saboda wasu dalilai
  • Bayan madatsun ruwan Dadin kowa da Lagdo sun cika sun batse, yanzu haka ana shirin bude su kafin su fashe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ta ba da sanarwar samun ambaliyar ruwa a kananan hukumomi tara na jihar sakamakon cikar dam din Dadinkowa da Lagdo.

Kananan hukumomin da ake fargabar za su samu ambaliya sun hada da Nguru, Bade, Karasuwa, Jakusko, Yusufari, Geidam,Tarmuwa, Bursari, Machina, Gujba da Fune.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Rundunar sojoji ta mika ta'azziyya Borno, za a taimaka wa jama'a

Ambaliya
An gargadi mazauna Yobe kan fargabar ambaliya Hoto: Mohammed Goje
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (SEMA) Dr. Muhammad Goje ne ya ba da sanarwar gargadin ranar Talata a Damaturu.

Yobe: An fara daukar matakin kare ambaliya

Shugaban hukumar SEMA na Yobe, Dr. Muhammad Goje ya shaidawa majiyar Legit cewa sanarwar da su ka bayar kan ambaliya kira ne saboda a dauki mataki kafin afkuwarsa.

Ya bayyana cewa gwamnatin Mai Mala Buni ta samar da matsugunai da jibge jami'anta a kananan hukumomin da aka ambata domin zama cikin shiri.

An saba ambaliya a jihar Yobe

Shugaban hukumar bayar da agajin ya ce dama a kan samu ambaliya idan an bude madatsun ruwan Lagdo, Challawa da Dadinkowa.

Ya bukaci mutane da su sanar da hukomomin gwamnati mafi kusa ko kuma ita kanta hukumar SEMA da zarar sun lura da alamun ambaliya.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Jami'an agaji sun maƙale a ruwa daga zuwa ceto mutane

Ambaliya ta kashe 'yan Boko Haram

A baya kun ji cewa ambaliyar ruwan da aka yi a jihar Borno ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan kungiyar Boko Haram da ke fakewa a dajin Sambisa su na kai hare-hare kan jama'a.

Rahotanni sun bayyana cewa ruwan ya yiwa yan Boko Haram muguwar illa, yayin da hakan ya tilasta masu sakin mutanen da su ka kama tare da ajiye su a dajin ba tare an yi masu laifi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.