Budurwa Ta yiwa Matashi Yankan Rago da Kwalba, Ya Mutu har Lahira

Budurwa Ta yiwa Matashi Yankan Rago da Kwalba, Ya Mutu har Lahira

  • Rundunar yan sanda a jihar Legas ta sanar da cewa wata budurwa ta yanka wuyan wani matashi da kwalba inda ya mutu har lahira
  • An ruwaito cewa matar da ake zargin ta samu sabani ne da matashin kafin ta dauki mummunan matakin kashe shi da kwalba
  • Yan sanda sun bayyana cewa a yanzu haka an dauki gawar matashin zuwa babban asibitin Yaba domin gwaji da binciken kwaƙof

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Ana zargin wata budurwa da yanka wani matashi da kwalba a yankin Ijegun a jihar Legas.

Yan sanda sun bayyana cewa a ranar 9 ga watan Satumban da muke ciki matar da ake zargin ta samu sabani da matashin.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: An tono gawar matashin da aka birne a daƙi, an kama mutum 1

Legas
An yanka matashi a Legas. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa rundunar yan sanda ta ce za ta gudanar da bincike a kan lamarin domin tabbatar da adalci.

Yadda aka yanka matashi da kwalba

Ana zargin wata budurwa mai suna Fatima Agboke a yankin Ijegun a jihar Legas da yanka wani matashi da kwalba a wuya.

Vanguard ta ruwaito cewa budurwar da ake zargi mai shekaru 19 ta samu sabani ne da matashin sai ta dauko kwalba ta fasa ta yanka shi a wuya.

Matashi mai suna Farouk Azeez ya rasu bayan yanka shi da kwalba da aka yi kuma ya kasance makwabcin matar ne.

Bayanin rundunar yan sandan Legas

Rundunar yan sanda a Legas ta tabbatar da cewa ta samu kiran gaggawa a lokacin da abin ya faru kuma ta samu Azeez kwance a cikin jini.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa da aka wayi gari da su a Maiduguri bayan ambaliya

Kakakin yan sanda a jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da cewa ana ƙoƙarin tafiya da Farouk Azeez zuwa babban asibitin Yaba ne ya rasu.

Benjamin Hundeyin ya tabbatar da cewa an kama matar da ake zargin kuma a yanzu haka ana gudanar da bincike kan lamarin.

Soja ya harbe matashi a jihar Benue

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suka fito daga jihar Benue na nuni da cewa an samu yamutsi bayan an zargi wani sojan Najeriya da harbe wani mutum.

An ruwaito cewa matasa sun nuna bacin rai yayin da suka so tayar da rikici bayan an dauki gawar mutumin da sojan ya bindige har lahira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng