Kwanaki da Alakantasa da 'Yan bindiga, Gwamna a Arewa Ya Tattago Aikin Kasuwar N3.6bn

Kwanaki da Alakantasa da 'Yan bindiga, Gwamna a Arewa Ya Tattago Aikin Kasuwar N3.6bn

  • Gwamantin jihar Zamfara ta kulla wata yarjejeniya da kamfanin Dhinat Global Ventures domin gina sabuwar kasuwa ta zamani a Gusau
  • Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Mannir Haidar ya sanar da cewa aikin gina kasuwar zamanin zai lakume Naira biliyan 3.6
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wata kungiya ta zargi Gwamna Dauda Lawal da hannu a ayyukan ta'addanci a Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya amince da kashe Naira biliyan 3.6 domin gina sabuwar k theasuwa ta zamani a Gusau, babban birnin jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Mannir Haidar ya fitar a Gusau a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kadu da ambaliyar ruwa a Maiduguri, ya ba Shettima sabon umarni

Gwamna Dauda Lawal ya amince a gina kasuwar N3.6bn a Gusau
Zamfara: Gwamna Dauda Lawal zai kashe N3.6bn a gina kasuwar zamani. Hoto: @daudalawal
Asali: Facebook

Gwamnati ta tattago aikin N3.6bn

Mannir Haidar ya ce an cimma matsayar gina sabuwar kasuwar ne a yayin taron majalisar zartarwa ta jihar da aka gudanar a Gusau, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, za a gudanar da aikin wanda zai lakume sama da Naira biliyan 3.6 a tsarin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da kamfanin Dhinat Global Ventures.

Radio Nigeria Kaduna ya rahoto cewa Alhaji Haidar ya jaddada kudurin gwamnati na kamfanin na kammala aikin cikin watanni 12.

Tasirin gina kasuwa a Gusau

Kwamishinan ya ci gaba da cewa majalisar zartarwar jihar ta bayar da shawarar cewa ayi amfani da filin tsohuwar kasuwar Gusau domin gina katafariyar kasuwar zamanin.

Sanarwar ta ce:

“Wannan shiri wani muhimmin bangare ne na dabarun gwamnati na bunkasa kasuwanci, tattalin arzikin da samar da yanayi mai kyau na harkokin kasuwanci a jihar.

Kara karanta wannan

"Ku taimake mu": Gwamna a Arewa ya sallami shugabannin kananan hukumomi 17

“Sabuwar kasuwar za ta zama cibiyar kasuwanci ta zamani ba da kuma ba da gudummawa wajen samar da ayyukan yi da inganta tattalin arzikin Zamfara baki daya."

Kwamishinan ya mika godiyar gwamnati ga al'ummar jihar bisa goyon bayan da suke ba ta, tare da fatan kammala aikin cikin nasara.

An alakanta gwamna da ta'addanci

A wani labarin, mun ruwaito cewa cibiyar yaki da 'yan fashin daji da ta'addanci (CABT) ta zargi Gwamna Dauda Lawal da daukar nauyin ayyukan 'yan ta'adda a Zamfara.

Cibiyar CABT ta kuma ce ta na zargin Gwamna Dauda Lawal da biyan yan ta'adda da miyagu N1.3bn domin cigaba da samun riba a harkar hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.