Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnatin Kano ta Shirya Yin Gwajin Kwaya ga 'Yan Takara

Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnatin Kano ta Shirya Yin Gwajin Kwaya ga 'Yan Takara

  • Gwamnatin Kano ta bakin hukumar zaben jihar (KANSEIC) ta dauki aniyar gudanar da gwajin shan miyagun kwayoyi ga 'yan takara
  • KANSEIC ta nemi hadin kan NDLEA domin yiwa 'yan takarar ciyaman da kansila gwajin kwaya kafin zaben kananan hukumomin jihar
  • Shugaban hukumar zaben, Farfesa Sani Malumfashi ya ce za su tabbatar ba a baiwa 'yan shaye shaye damar hawa mukaman siyasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Hukumar zaben Kano (KANSEIC) za ta gudanar da gwajin kwaya kan 'yan takarar ciyaman da kansila da za su fafata a zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe.

Shugaban hukumar, Farfesa Sani Malumfashi ne ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da ya kai hedikwatar hukumar NDLEA ta Kano a ranar Talata.

Kara karanta wannan

NNPP ta fito da mace a matsayin 'yar takarar shugaban karamar hukumar Kano

Gwamnatin Kano ta yi shirin gwajin kwaya ga 'yan takarar ciyaman da kansila
Hukumar zaben Kano za ta yi gwajin kwaya ga 'yan takarar ciyaman da kansila. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Facebook

Gwajin kwaya ga 'yan takara a Kano

Farfesa Malumfashi ya jaddada cewa hukumar ta shirya yin gwajin kwaya kan ‘yan siyasar da suka tsaya takarar ciyaman da kansila a zaben jihar, inji rahoton The Punch.

Hukumar KANSEIC ta kara da cewa ta na neman hadin kan hukumar ta NDLEA wajen gudanar da gwajin kwayoyin kan ‘yan takarar a dukkanin jam’iyyun siyasar jihar.

Bayan kammala gwajin, hukumar ta ce za ta duba sakamakon domin tantance ko dan siyasa ya cancanci tsayawa takara ko akasin hakan tare da daukar mataki na gaba.

Farfesa Malumfashi ya ci gaba da cewa hukumar KANSEIC ta dukufa wajen ganin an dakile masu shaye-shayen miyagun kwayoyi daga gudanar da mulki a kananan hukumomi.

"Amfanin gwajin kwaya" - KANSEIC

Shugaban hukumar zaben ya ce gudanar da gwajin kwaya kan 'yan takarar na da matukar muhimmanci yana mai cewa:

Kara karanta wannan

'Yan takarar NNPP 20 na ta'ammali da kwayoyi a kano? NDLEA ta yi karin haske

“Dora 'yan shaye-shaye a mukaman shugabancin kananan hukumomi zai kara tabarbarewar shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar.
"Hakazalika, lamarin zai iya yin tasiri ga kudin baitul malin kananan hukumomi ta fuskar karuwar masu shaye-shayen miyagun kwayoyi."

Kwamandan NDLEA na Kano, Abubakar Ahmad a tabbatar wa KANSEIC cewa rundunarsa za ta ba da dukkanin goyon baya domin gudanar da sahihin zabe a jihar.

NDLEA ta fara gwajin kwaya

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NDLEA ta ce ta samu 'yan takarar jam'iyyar NNPP 20 da laifin shan miyagun kwayoyi bayan gaza tsallake gwajin da aka yi masu.

Jam'iyyar NNPP dai ta gabatarwa NDLEA da sunayen 'yan takararta da za su fafata a zaben kananan hukumomin jihar mai zuwa domin a yi masu gwajin kwaya bisa umarnin KANSEIC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.