Kano: Matashi Ya Yi Garkuwa da Kaninsa 'Dan Shekara 4, Ya Nemi Fansar Naira Miliyan 10
- Rundunar yan sandan jihar Kano ta yi nasarar cafke wani matashi da ya jagoranci sace wani 'dan kanwar mahaifiyarsa
- Muhammad Nasir Jamilu, dan shekaru 4 ya gamu da sharrin zamani bayan yayansa, Hisbullah Salisu ya sa an dauke shi
- An sace yaron a gidansu da ke Sharada, aka nemi fansar N10,000,000 kuma tuni aka fara da basu N300,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Rundunar yan sandan jihar Kano ta bayyana nasarar cafke wasu matasa uku bisa zargin sace wani Muhammad Nasir Jamilu mai shekaru hudu.
Matasan sun sace Muhammad ne a gidansu da ke Sharada sannan aka kai shi garin Gwarzo, karkashin jagorancin yayansa, Hisbullah Salisu.
A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce Hisbullah ya samu taimakon mutum biyu wajen satar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutum
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa rundunar yan sandan Kano ta kama wasu matasa; Hisbullahi Salisu, Hassan Ali Rabiu da Hassan Aliyu kan zargin satar yaro.
Matasan sun amsa cewa sun dauke yaron ne tare da barazanar kashe shi idan ba a biya fansar N10,000,000 ba, tuni aka fara ba su N300,000.
"An ceto yaro a Kano," Yan sanda
Rundunar yan sandan Kano ta bayyana cewa an ceto yaro mai shekaru hudu mai suna Muhammad da aka sace a Sharada.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an mika yaron asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda aka tabbatar da lafiyarsa.
Yan sanda sun ceto matashiya
A baya mun ruwaito cewa rundunar yan sandan Kano da hadin gwiwa da yan sandan Kaduna sun yi nasarar cafke masu garkuwa da mutane a dajin Kaduna.
Kakakin rundunar yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an sace matashiyar mai shekaru 20 a Zarewa da ke karamar hukumar Rogo a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng