Karshen Bello Turji Ya Zo, Babban Hafson Tsaro Ya Fadi Lokacin Cafke Jagoran 'Yan Bindiga

Karshen Bello Turji Ya Zo, Babban Hafson Tsaro Ya Fadi Lokacin Cafke Jagoran 'Yan Bindiga

  • Babban hafsan tsaro na ƙasa Christopher Musa ya sha alwashi kan Bello Turji wanda ya addabi mutanen jihar Zamfara
  • Janar Christopher Musa ya bayyana cewa nan da ɗan ƙanƙanin lokaci za a cafke jagoran 'yan ta'addan da ke Arew ta yamma
  • Ya kuma ƙara da cewa za a magance matsalar harajin da Bello Turji da sauran ƴan binɗiga suka ƙaƙabawa mutanen Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban hafsan tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa ya sha alwashin cafke ƙasurgumin ɗan ta'adda Bello Turji.

Bello Turji na ɗaya daga cikin shugabannin ƴan bindiga da ake fargaba a yankin Arewa maso Yamma, wanda ya daɗe yana ta'addanci kan al'ummar jihar Zamfara

Kara karanta wannan

A ƙarshe Shugaba Tinubu ya faɗi ayyukan da yake yi da kudin tallafin man fetur

CDS ya sha alwashin cafke Bello Turji
Janar Christopher Musa ya sha alwashin cafke Bello Turji Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa Janar Christopher Musa ya sha wannan alwashin ne yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Talata a birnin Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanan nan Bello Turji ya sanya harajin N30m ga mazauna ƙauyen Moriki a jihar Zamfara sakamakon kashe masa shanu da jami'an tsaro suka yi.

Me hafsun tsaro ya ce kan Bello Turji

Babban hafsan tsaron ya bayyana Bello Turji a matsayin 'mahaukacin mutum' kuma ya sha alwashin cewa za a kama shi cikin ƙanƙanin lokaci, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Janar Christopher Musa ya kuma bayyana cewa za a magance matsalar harajin da Bello Turji da sauran ƴan bindiga suka sanya.

"A kan batun Bello Turji, kamar yadda na ce, shi mahaukacin mutum ne kawai wanda yake jin iko, amma zan iya cewa lokaci kawai ake jira."

Kara karanta wannan

Manyan hafsoshin tsaron Najeriya sun fara bayani kan matsalar tsaro, bayanai sun fito

"Lokaci kawai mu ke jira, za mu cafke shi kuma ina tabbatar muku cewa za mu cafke shi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci."

- Janar Christopher Musa

Malami ya caccaki Matawalle kan ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji malamin addinin musuluncin nan Sheikh Murtala Bello Asada ya yi magana kan shirin Bello Matawalle na yakar miyagun ƴan bindiga.

Shehin malamin ya caccaki gwamnati inda ya ce ba da gaske ta ke yi ba saboda yadda suka sanarwa duniya shirinsu na yin fito na fito da ƴan bindigan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng