Dara Ta ci Gida: An Garkame Tsohon Alkalin Kotun Shari'ar Musulunci a Kaduna

Dara Ta ci Gida: An Garkame Tsohon Alkalin Kotun Shari'ar Musulunci a Kaduna

  • Wani tsohon alkalin kotun shari'ar Musulunci ya shiga hannu kan zargin cin zarafin matar aure da ta ke makauniya
  • Wanda ake zargib, Mahmud Shehu an gurfanar da shi a gaban kotun majistare da ke Zaria a jihar Kaduna
  • Daga bisani alkalin kotun, Lukman Sidi ya bukaci wanda ake zargin ya biya belin N50,000 da kawo wanda zai tsaya masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - An cafke tsohon alkalin kotun shari'ar Musulunci a jihar Kaduna kan zargin cin zarafi.

Ana zargin Mahmud Shehu da zargin cin zarafin wata matar aure da ta ke makauniya a birnin Zaria da ke jihar.

An daure tsohon alkalin kotun shari'ar Musulunci a Kaduna
Alkalin kotun shari'ar Musulunci ya shiga hannu kan zargin cin zarafin matar aure. Hoto: Legit.
Asali: Original

Mene ake zargin tsohon alkalin kotun Musulunci

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin hari da asuba, sun kashe bayin Allah a Arewa

An gurfanar da Mahmud ne a yau Talata 10 ga watan Satumbar 2024 a kotun majistare da ke birnin Zaria a Kaduna, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Adamu Abubakar ya ce ana zargin Shehu da cin zarafi da kuma wuce gona da iri.

Adamu ya ce laifin da ya aikata ya sabawa kundin laifuffukan jihar Kaduna na shekarar 2017, cewar rahoton Vanguard.

Ya ce a ranar 6 ga watan Satumbar 2024 wani mai suna Garba Adda'u ya kai korafi ofishin yan sanda kan laifin Mahmud Shehu.

Har ila yau, ya ce Shehu ya shiga gidansa inda ya kulle kofa tare da cin zarafin matarsa da ba ta gani da masu aikinta guda biyu.

Wane martani wanda ake zargin ya yi?

Sai dai wanda ake zargin ya musanta korafe-korafen da ake yi masa da cewa bai san da su ba kwata-kwata.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke budurwar wani rikakken ɗan bindiga a Taraba, bayanai sun fito

Alkalin kotun, Mai Shari'a, Lukman Sidi ya ce tsohon alkalin zai biya kudin beli har N50,000 da kuma wanda zai tsaya masa.

Sidi daga bisani ya dage cigaba da sauraran karar har zuwa ranar 8 ga watan Oktoban 2024 da muke ciki.

Yan bindiga sun hallaka mutane a Kaduna

Kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun hallaka mutum biyar tare da sace wasu da dama a harin da suka kai a ƙauyen Kallah Afogo a garin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.