Bello Turji Ya Cafke Ƴan Siyasa da Mutane 15, Ya Sanya Gari cikin Ɗar Ɗar kan Haraji

Bello Turji Ya Cafke Ƴan Siyasa da Mutane 15, Ya Sanya Gari cikin Ɗar Ɗar kan Haraji

  • Ƙasurgumin ɗan bindiga mai garkuwa da mutane, Bello Turji ya sanya mutanen Moriki cikin zaman ɗar ɗar bayan sun gaza biyan haraji
  • Bello Turji ya sanyawa mutanen Moriki haraji ne bayan ya yi zargin cewa sojojin Najeriya da aka tura garin sun kashe masa shanu
  • Haka zalika Bello Turji ya yi garkuwa da yan siyasa kimanin 15 a garin yayin da yake jira su tattara harajin da ya daura musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Mutanen Moriki a jihar Zamfara sun shiga fargaba yayin da suka gaza biyan harajin da Bello Turji ya daura musu.

Bello Turji ya daura musu harajin N50m saboda kashe masa shanu da aka yi amma suka roke shi ya rage musu zuwa N30m.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace Bello Yabo? Shehi ya yi maganar 'garkuwa' da shi da 'kamen' DSS

Zamfara
An rude a Zamfara bayan gaza biyan harajin Bello Turji. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Bello Turji ya yi zargin cewa mutanen Moriki sun haɗa kai da yan sanda ne wajen kashe masa shanu.

Ana zaman ɗar ɗar kan tsoron harin Turji

Wa'adin da Bello Turji ya sanya wa mutanen Moriki domin biyan harajin N30m ya cika a ranar Litinin amma sun gaza biyan kudin.

Mutanen garin sun shiga tashin hankali domin Bello Turji ya ce idan suka gaza biyan kudin za su hadu da fushinsa.

Turji ya sace mutane kimanin 15 a Moriki

Duk da sanya musu haraji, dan ta'adda Bello Turji ya yi garkuwa da yan siyasa da masu amfani da 'yan gwagwarmaya kimanin 15 a garin Moriki.

Lauya mai fashin baki, Audu Bulama Bukarti ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya koka da sace mutane a asibitin Kaduna, ya fadi abin da ake bukata

Sojoji sun ce kar a biya harajin Turji

Kwamandan sojoji a garin Moriki ya yi kira ga mutane garin a kan kar su biya harajin da dan ta'addar ya daura musu.

Sai dai duk da haka mutanen suna cikin dar dar kasancewar sun gaza biyan kudin kuma ba a san mummunan shirin da Bello Turji ke kulla musu ba.

Za a ba mutane damar mallakar bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya nuna takaici kan yadda yan bindiga ke kashe mutane da sace su.

Dikko Umaru Radda ya ce a shirye yake ya ba mutane bindigogi domin su rika fafatawa da yan ta'adda masu garkuwa da mutane a Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng