Turji Ya Ba Da Umarnin Tsare Mazauna Zamfara Kan Rashin Biyan Naira Miliyan 20 Na 'Harajin Kariya'

Turji Ya Ba Da Umarnin Tsare Mazauna Zamfara Kan Rashin Biyan Naira Miliyan 20 Na 'Harajin Kariya'

  • Hatsabibin shugaban yan fashin Dajin Zamfara, Bello Turji ya tsare wasu mutanen garin Moriki kan rashin biyan 'harajin kariya'
  • Wani mazaunin garin Moriki, Sani, ya ce Turji ya umurci su tara masa Naira miliyan 20 cikin sati biyu idan suna son kada a kawo musu hari kuma su samu daman zuwa gonaki
  • Mutanen garin sun yi karo-karo suka hada naira miliyan 10.8 suka kai masa, amma hakan ya fusata shi ya rike biyar cikin yan sakon

Jihar Zamfara - An rahoto cewa Bello Turji, hatsabibin shugaban yan bindiga ya tsare wasu mazauna garin Moriki biyar a karamar hukumar Zurmi.

An tsare wadanda abin ya shafa ne bayan sun kai masa kudi Naira miliyan 10.5 na 'harajin kariya' da ya kakabawa garinsu, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Turji da sojoji
Turji Ya Ba Da Umarnin Tsare Mazauna Zamfara Kan Rashin Biyan Naira Miliyan 20 Na 'Harajin Kariya'. Hoto: @VanguardNG/@GuardianNG.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan makonni da suka gabata, Turji ya kakabawa garin Moriki da ke kilomita 33 kan hanyar Kaura Namoda zuwa Shinkafi biyan Naira miliyan 20 a matsayin 'harajin kariya'.

Shugaban yan bindigan ya ce idan za su iya hada kudin cikin makonni biyu, ba za a kawo musu hari ba kuma kowanne manomi zai iya zuwa gonarsa ba tare da fargaba ba, rahoton Premium Times.

Mazaunin garin Moriki ya magantu kan yadda lamarin ya faru

Wani mazaunin garin, Sani Moriki ya ce bayan ya kakaba mana harajin mun yi taro don ganin yadda za mu hada kudin saboda sanin abin da zai faru idan muka yi bin umurninsa.

A cewar Sani:

"Mun bada shawarar kowanne gida a garin ya biya N6500 idan muka hada za mu samu naira miliyan 20 mu bashi kafin karewar wa'adin.

Kara karanta wannan

Bayan Sauyin Launi, Buhari Ya Nuna Inda Sababbin Kudin da Aka Yi Suka Bambanta

"Mun iya tara naira miliyan 10.6 saboda wasu gidajen ba su biya ba. Mun yi amfani da N100,000 muka siya musu sigari, burodi, lemun kwalba da katin waya kamar yadda suka umurta.
"An tura mutane bakwai a garin su kai kudin a wurin da aka yi yarjejeniya kusa da Kasayawa, wani gari da ke kilomita 1 gabashin Moriki. Bayan tawagar sun isa wurin, yaran Turji su 17 suka taho suka bukaci kudin da sauran kayan da muka kawo."

Turji ya fusata bayan gano kudin bai cika Naira miliyan 20 ba

Ya cigaba da cewa:

"Amma, da aka sanar da Turji cewa kudin da aka kawo naira miliyan 10.2 ne ba miliyan 20 kamar yadda aka yi yarjejeniya ba, ya fusata ya umurci yaransa su tsare biyar cikin mutum bakwai da suka kai sakon. Ya umurci su kai mutanen wani sansaninsa da ke dajin Jirari da ke kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi. Duk da cewa biyu cikinsu sun tsere sun dawo da safiyar yau.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Yana Zugo Gwamnoni 36 Su Taya shi Yaki da Gwamnatin Najeriya kan Haraji

"Yanzu muna zaman dar-dar kuma mun fara kokarin tuntubarsa mu bashi sauran naira miliyan 10. Muna cikin babban matsala a matsayin al'umma."

Martanin yan sanda

Kakakin yan sandan jihar SP Muhammad Shehu ya ce zai bincika ya gano ainihin abin da ya faru.

Shugaban Yan Bindiga, Bello Turji, Ya Mayar Da Martani Kan Harin Jirgin Sojin Najeriya

A wani rahoton na daban, Bello Turji, shugaban yan fashin daji a Zamfara ya ce cin amana ne faramakin da sojoji suka kai sansaninsa.

Kamar yadda The Cable ta rahoto, luguden wutar da sojojin saman Najeriya suka yi ya yi sanadin mutuwar yan bindiga 10 a sansanin Turji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel