"Mun San da Baragurbi cikinmu:" Rundunar Sojoji Ta Fadi Kokarinta kan Rashin Tsaro

"Mun San da Baragurbi cikinmu:" Rundunar Sojoji Ta Fadi Kokarinta kan Rashin Tsaro

  • Rundunar sojojin kasar nan ta bayyana cewa ta na bakin kokarinta wajen magance matsalar tsaro da ta addabi Najeriya
  • Babban hafsan tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka jim kadan bayan tattaunawa da takwarorinsa
  • Babban hafsan tsaro kan ayyuka, Manjo Janar Emeka Onumajuru ya ce su na sane da wasu bata gari cikin rundunar sojojin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Rundunar sojojin kasar nan ta ba yan Najeriya tabbacin cewa ta na iya kokarinta wajen magance matsalolin tsaron da ake fama da su.

Babban hafsan tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka bayan ya gana da sauran jagororin hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya koka da sace mutane a asibitin Kaduna, ya fadi abin da ake bukata

Jamar
Sojoji sun ce ana kokarin magance rashin tsaro Hoto: Katsina State Government
Asali: Facebook

TVC News ta wallafa cewa Janar Musa ga kara da cewa dakarun sojin kasar nan sun samu manya-manyan nasarori a yakin da su ke yi da ta'addancin da yan ta'adda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za mu yaki yan bindiga" - Rundunar soja

Rundunar sojojin kasar nan ta bayyana cewa dole sai ta ribanya kokarinta na yaki da yan ta'adda da ta'addanci.

Babban hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa ne ya bayyana haka, inda ya ce su na aiki da sauran hukumomin tsaro.

Rundunar sojoji ta san da bata gari cikinta

Babban hafsan tsaro kan ayyuka na rundunar sojojin kasar nan, Manjo Janar Emeka Onumajuru ya ce su na sane da cewa akwai bara gurbi a cikinsu. Rundunar sojojin ta nemi hadin kai domin tabbatar da an samu nasara a yakin da ake yi da wadanda ke haddasa rashin zaman lafiya a kasar nan.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano sun tashi da takaici, an tsinci jaririya a ƙarkashin tayar mota

Sojoji sun yi nasara kan yan ta'adda

A wani labarin kun ji cewa jami'an sojojin kasar nan sun samu nasarar damke wasu mata da aka kama su na sayen kayayyakin da ake zargin za su kai wa yan ta'adda a Kaduna.

Dakarun sun bi sawun matan guda biyu zuwa kasuwa bayan an samu bayanan sirri da ke nuna cewa su na mika bayanai da sayen kayan da yan bindiga ke bukata a karamar hukumar Kachia.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.