Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya Sun Fara Bayani kan Matsalar Tsaro, Bayanai Sun Fito

Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya Sun Fara Bayani kan Matsalar Tsaro, Bayanai Sun Fito

  • Manyan hafsoshin tsaron Najeriya sun taru a Abuja domin yi wa ƴan ƙasa karin haske kan matsalar tsaron da ake fama da ita
  • Rahotanni sun nuna taron na gudana ne a hedkwatar tsaro da ke Abuja ƙarƙashin jagorancin babban hafsan tsaro Christopher Musa
  • Wannan na zuwa ne kusan mako guda bayan ƙaramin ministan tsaro ya jagoranci shugabannin hukumomin tsaro zuwa Sakkwato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka manyan hafsoshin tsaro. Najeriya na jawabi kan halin matsalar tsaro da ake fama da ita a ƙasar nan.

Taron dai na gudana ne ƙarƙashin jagorancin hafsan hafsoshin tsaron ƙasar nan, Janar Christopher Musa a hedkwatar tsaro da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Karshen Bello Turji ya zo, babban hafsan tsaro ya fadi lokacin cafke jagoran 'yan bindiga

Christopher Musa.
Hafsoshin tsaro sun yi ƙarin haske kan halin rashin tsaron da ake fama a Najeriya Hoto: @DefenceinfoNG
Asali: Facebook

Manyan hafsoshin da suka hallara a DHQ

Waɗanda suka halarci wurin sun haɗa da wakilin babban hafsan sojojin ƙasa, wakilin hafsan sojojin sama da wakilin hafsan sojojin ruwa, The Nation ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun haɗa da wakilin sufetan ƴan sanda na ƙasa, shugaban hukumar shige da fice, Kemi Nandap da kwanturola janar na hukumar kula da gidajen gyaran hali,

Kazalika manyan jami'an hedkwatar tsaro da sauran hukumomin tsato sun hallara a wurin yau Talata, 10 ga watan Satumba, 2024.

Hafsoshin tsaro sun tare a Sokoto

A makon jiya ƙaramin ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle ya jagoranci hafsoshin tsaro zuwa jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Matawalle da shugabannin tsaron sun tare a jihar ne bisa umarnin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu domin maganin ƴan bindiga waɗanda suka addabi al'umma.

Shugaba Tinubu ya umarci manyan jami'an tsaron su tafi Sakkwato ne bayan wasu ƴan bindiga sun halaka sarkin Gobir, Isah Muhammad Bawa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin hari da asuba, sun kashe bayin Allah a Arewa

Bayan haka ne a yau hafsoshin tsaron suka taru a hedkwstar tsaro domin yi wa ƴan Najeriya karin haske kan halin da ake ciki game da tsaro, Punch ta ruwaito.

DHQ ta faɗi nasarorin sojoji a mako guda

A wani rahoton kun ji cewa Sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta'adda 1,166 tare da kama wasu 1,096 a watan Agusta, 2024 a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Mai magana da yawun hedkwatar tsaro DHQ, Edward Buba ne ya sanar da haka, ya ce sojoji sun kashe hatsabiban ƴan bindiga a Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262