Bidiyon Bello Asada: Malaman Musulunci Sun Yi Gargadi, Sun bi Bayan Matawalle, Tinubu

Bidiyon Bello Asada: Malaman Musulunci Sun Yi Gargadi, Sun bi Bayan Matawalle, Tinubu

  • Gamayyar malaman Musulunci daga Arewacin Najeriya sun goyi bayan yaki da ta'addanci na gwamnatin Bola Tinubu
  • Kungiyar Concerned Scholars for Peace and Development (CSPD) ta ce akwai masu siyasantar da lamarin tsaro a Arewa maso Yamma
  • Ta kuma shawarci Bola Tinubu da ka da ya bari a kawar masa da hankali wurin yaki da ta'addanci a kasar baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wata kungiyar malamai masu son zaman lafiya ta goyi bayan Bola Tinubu game da yaki da yan bindiga.

Kungiyar Concerned Scholars for Peace and Development (CSPD) ta bukaci ba shugaban hadin kai wurin dakile ta'addanci.

Malaman Musulunci sun goyi bayan Matawalle da Tinubu a yaki da ta'addanci
Kungiyar Malaman Musulunci ta gargadi masu siyasantar da rashin tsaro tare da goyon bayan Tinubu da Matawalle. Hoto: Dr. Bello Matawalle, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Ta'addanci: Kungiya ta goyi bayan Tinubu, Matawalle

Kara karanta wannan

'Yan Kudu da Arewa sun hada kai, sun tunkari Tinubu kan tsadar man fetur

Shugaban kungiyar, Dr. Zaharadden Mohammed Kabir shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da Tribune ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Kabir ya gargadi masu kokarin zagon kasa da kokarin kawar da hankalin Ministan tsaro, Bello Matawalle da jami'an tsaro.

Ya ce wasu na kokarin siyasantar da rashin tsaron da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, cewar rahoton Vanguard.

Kungiya ta ba Tinubu shawara kan ta'addanci

"Kungiyar malaman Musulunci da ke son zaman lafiya ta yi Allah wadai da masu kokarin siyasantar da rashin tsaro a Arewa maso Yamma."
"Muna bukatar Shugaba Bola Tinubu da ka da ya bari a kawar masa da hankali wurin kokarin fatattakar yan bindiga a kasar."
"Wannan martani ne ga bidiyon da wani malamin Musulunci ya ke zargin gwamnatin Tarayya da daukar nauyin ta'addanci."

Kara karanta wannan

DSS ta tsorata, ta saki Ajaero mintuna kafin wa'adin kungiyar NLC ya cika

- Cewar sanarwar

Kungiyar ta ce nan gaba kadan wasu za su sake bulla yayin da ake cigaba da kai farmaki kan yan bindiga inda ta bukaci Tinubu ya mayar da hankali kan abin da ya saka a gaba.

Malamin Musulunci ya zargi Matawalle da ta'addanci

Kun ji cewa wani malamin Musulunci a jihar Sokoto ya zargi karamin Ministan tsaro, Bello Matwalle da hannu a ta'addanci.

Sheikh Murtala Bello Asada ya ce tabbas Matawalle ya siyawa manyan shugabannin yan bindiga motoci ciki har da Bello Turji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.