"Akwai Barazana": Ribadu Ya Bayyana Hanya 1 na Inganta Darajar Naira

"Akwai Barazana": Ribadu Ya Bayyana Hanya 1 na Inganta Darajar Naira

  • Hadimin shugaban kasa a bangaren tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya bayyana hanyar farfado da tattalin arziki a Najeriya
  • Nuhu Ribadu ya ce dole sai an dakile matsalar fasa kwaurin mai zuwa ketare kafin dawo da darajar Naira da tattalin arziki
  • Ya ce babu kasa da ke shan fama da wannar matsalar a ganinsa kamar Najeriya inda ya ce dole a dauki matakin gaggawa a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Mai ba da shawara ga Bola Tinubu a harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya fadi hanyar inganta daraar Naira.

Ribadu ya ce dole sai an dakile matsalolin fitar da mai a Najeriya ba bisa ka'ida ba kafin cimma wannan nasara.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano sun tashi da takaici, an tsinci jaririya a ƙarkashin tayar mota

Nuhu Ribadu ya yi magana kan yadda za a daga darajar Naira
Mallam Nuhu Ribadu ya ce dole a kawo karshen satar mai kafin daga darajar Naira. Hoto: Nuhu Ribadu.
Asali: Facebook

Ribadu ya kawo hanyar inganta Naira

Tsohon shugaban EFCC ya fadi haka ne a jiya Litinin 9 ga watan Satumbar 2024 yayin wani taro da jami'an Kwastam, cewar rahoton Daily Trust.

Ribadu ya ce fitar da mai ketare daga Najeriya ba bisa ka'ida ba yana da matukar tasiri wurin rashin daidaiton darajar Naira.

Ya ce hakan yana matukar tarwatsa Najeriya har ma da jami'an tsaronta saboda wasu tsiraru da ke cin riba.

Har ila yau, Ribadu ya ce idan har ba a kawo karshen matsalar ba za ta kassara Najeriya saboda kamar cutar daji take tana cin kasar a hankali.

Ribadu ya koka kan yawan satar mai

"Muna shan wahala saboda fitar da mai ketare ba bisa ka'ida ba, idan muna son kawo karshen matsalar tattalin arziki dole mu dakile hakan."

Kara karanta wannan

"Mutane za su wahala": Atiku ya yi adawa da shirin kara hajari, ya gargadi Tinubu

"Hakan yana da matukar wahala saboda kamar cutar daji ta ke tana cinye komai, ta na lalata kasar da jami'an tsaronta saboda wasu da ke cin ribar hakan."
"Ba na tsammanin akwai wata kasa da ke shan fama game da haka fiye da Najeriya, dole mu dakile matsalar idan ba haka ba darajar Naira ba za ta farfado ba."

- Nuhu Ribadu

Ta'addanci: Gwamnati ta na zargin mutane 300

Kun ji cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya yi bayani kan yan ta'adda da aka kama a Najeriya.

Ribadu ya bayyana irin yadda gwamnatin Bola Tinubu ke kokarin ganin an yanke hukunci ga dukkan masu laifin da aka kama da zargi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.