Sanusi II Ya Roki Al’umma Alfarma game da Attajiran Kano, Dangote da BUA
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya roki ubangiji ya hada kan attajiran jihar guda biyu domin kawo mata cigaba
- Sanusi II ya kuma roki al'umma su dage da addu'o'i domin Allah ya hada kan attajiran Kano, Aliko Dangote da Abdussamad Rabiu
- Basaraken ya ce duk mai neman kawo rigima tsakanin attajiran na Kano ba son cigaban jihar ya ke yi ba ko kadan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya roki al'umma alfarmar addu'o'i ga attajiran jihar.
Sanusi II musamman ya bukaci a yi addu'o'i ga Aliko Dangote da Abdussamad Rabiu domin Allah ya hada kansu.
Sanusi II ya yi addu'a ga Dangote & BUA
Sarkin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Muhammadu Sanusi II Sanippets ya wallafa a shafin X.
A cikin faifan bidiyon, Sarkin ya yi addu'ar Allah ya hada kansu domin samun cigaban jihar baki daya.
Sanusi II ya ce duk mai neman hada rigima ko son rikici tsakanin attajiran guda biyu ba son cigaban jihar Kano ya ke ba.
Sanusi II ya roki addu'a ga attajiran Kano
"Wadannan yan kasuwan namu guda biyu a yau a Afirka babu wanda ya kai su kudi, muna rokon yan uwa mu yi addu'a Allah ya hada zukatansu."
"Duk wanda ya ke neman fitina tsakanin Aliko Dagote da Abdussamad Rabiu wadanda yan Kano ne kuma suka fi kowa arziki, jihar ya ke son ya cutar."
"Duk mai son fitina tsakaninsu, ka da Allah ya ba shi nasara, su kuma Allah ya karkato zukatansu su waiwayi Kano su kawo mata cigaba."
- Muhammadu Sanussi II
Sarkin Potiskum ya ziyarci Muhammdu Sanusi II
Kun ji cewa Sarkin Potiskum da ke jihar Yobe, Umar Bauya ya kai ziyarar goyon baya ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Basaraken ya ce ya zo fadar Sanusi II ne domin yin mubaya'a da nuna goyon baya a gare shi da mutanensa baki daya.
Sarkin ya roki Sanusi II da ya ba da gudunmawarsa wurin karasa gina masallacin Juma'a da suka faro shekarun baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng