NLC Ta Na Son Jiƙawa Tinubu Aiki, Ta Bukaci Rage Kudin Fetur a Jerin Bukatu 4
- Kungiyar kwadago ta yi magana bayan shiga ganawar gaggawa da ta yi a kan kama shugabanta, Kwamared Joe Ajaero
- Yan kwadago sun fitar da sababbin bukatu hudu ga gwamnatin tarayya ciki har da rage kudin fetur da aka kara a makon jiya
- A yau ne jami'an DSS suka kama shugaban NLC na kasa, Ajaero yayin da yake kokarin tafiya Birtaniya domin taron kwadago
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta yanke matsaya bayan ta shiga taron gaggawa a birnin tarayya Abuja.
Yan kwadago sun bayyana sababbin bukatu da suke so gwamnatin tarayya ta cika masu cikin gaggawa.
Legit ta tatttaro bayanan da yan kwadago suka yi ne a cikin wani sako da kungiyar ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bukatun yan kwadago 4
- Kungiyar kwadago ta bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta dawo da kudin man fetur da aka kara a cikin makon da ya wuce.
- Yan kwadago sun bukaci jami'an DSS su gaggauta sake shugabansu, Kwamared Joe Ajaero ba tare da wani sharadi ba.
- Haka zalika NLC ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta tabbatar da fara biyan mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000.
- A ƙarshe, kungiyar kwadago ta bukaci gwamnatin tarayya ta rage kudin wutar lantarki da aka kara a Najeriya ba bisa ka'ida ba
NLC za ta yi wani taron gaggawa
Kungiyar kwadago ta sanar da cewa a gobe Talata za ta yi taro na musamman a birnin tarayya Abuja da misalin karfe 9:00 na safe.
Ana sa ran cewa a gobe ne kungiyar kwadago za ta fadi matakin da za ta dauka idan gwamnatin tarayya ba ta biya mata bukatunta ba.
NLC ta koka ka zargin cin zarafi
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kwadago ta yi Allah wadai da kama shugabanta, Joe Ajaero da jami'an DSS suka yi a birnin tarayya Abuja.
Yan kungiyar NLC sun bayyana cewa cin zarafi da barazana da gwamnatin tarayya ke musu dole a kawo karshensa a Najeriya cikin gaggawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng