Ziyarar Tinubu Zuwa Kasar Sin Ta Yi Riba, Ya Rattaba Hannu kan Aikin $3.3bn

Ziyarar Tinubu Zuwa Kasar Sin Ta Yi Riba, Ya Rattaba Hannu kan Aikin $3.3bn

  • Ziyarar da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi zuwa kasar Sin ta yi riba bayan da kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar dala biliyan 3.3
  • An rahoto cewa Najeriya da kasar Sin sun rattaba hannu kan yarjejeniyar bunkasa masana'antar karfen Brass da Methanol da ke Bayelsa
  • An bayyana yarjejeniyar a matsayin sake jaddada kudurin kasashen biyu na zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da karfafa dangantaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sin - Najeriya da kasar Sin sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar dala biliyan 3.3 domin bunkasa masana'antar karfen Brass da Methanol da ke jihar Bayelsa.

Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar kudi ta tarayya, Mohammed Manga ne ya sanar da hakan a daren jiya.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano sun tashi da takaici, an tsinci jaririya a ƙarkashin tayar mota

Najeriya ta kulla jarjejeniyar dala biliyan 3.3 da kasar Sin
Najeriya da kasar Sin sun rattaba hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 3.3 domin bunkasa masana'antu. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Najeriya da Sin za sun kulla yarjejeniya

A cikin wata sanarwa da jaridar Vanguard ta gani, Mohammed Manga ya ce, an rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a gefen taron kasashen Afrika da Sin da ke gudana a birnin Beijing.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manga ya ce ana sa ran yarjejeniyar za ta bunkasa masana'antu a Najeriya da kuma samar da muhimman ayyukan yi ga 'yan kasar.

Daraktan ya bayyana yarjejeniyar a matsayin sake jaddada kudurin kasashen biyu na zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki, da karfafa dangantakar dake tsakaninsu.

Najeriya da Sin sun karfafa dangantaka

Jaridar The Punch ta rahoto sanarwar ta kara da ce:

"Taron farko na hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Najeriya, ya kafa tsarin alakar da ba a taba yin irinsa ba a tsakanin kasashen biyu."

Ministan kudi da tattalin arziki, Mr. Wale Edun, ya jaddada cewa Shugaba Bola Tinubu ya himmatu wajen samar da yanayin kasuwa mai kyau da zai jawo masu zuba jari a kasar.

Kara karanta wannan

An rasa muhalli da dukiya: Jihohin Arewa da ambaliyar ruwa ta yiwa barna a 2024

An ce, bunkasa ababen more rayuwa a matsayin ginshikin hadin gwiwar Sin da Najeriya shi ne babban abin da aka fi maida hankali a kai a taron.

Tinubu ya shilla kasar Sin

Tun da fari, mun rahoto cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya shilla zuwa kasar Sin watau China domin halartar taron kasashen Afrika da Sin da ke gudana a birnin Beijing.

An rahoto cewa shugaban kasar ya shirya karfafa dangantakar da ke kasashen Najeriya da Sin da kuma nemowa Najeriya masu zuba jari a masana'antu da makamashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.