"Har da Kai a Ciki": APC Ta Caccaki Tsohon Jigonta kan Sukar Buhari da Tinubu
- Kalaman da tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa, Salihu Lukman, ya yi ba su yi wa jam'iyyar daɗi ba
- Jam'iyyar APC ta yi martani kan kalaman nasa inda ta bayyana cewa shi ma yana da alhaki a iƙirarin da ya yi
- Ta ce a matsayinsa na mai faɗa a ji, ya taimaka wajen ba da shawarwari kan shirye-shirye da tsare-tsaren gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta mayar da martani kan kalaman Salihu Mohammed Lukman, wanda ya ce shekara tara da APC ta yi tana mulki sun fi muni kan shekara 16 na PDP.
Salihu Lukman ya caccaki tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da kuma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ya zarge su da kasa cika alƙawuran da suka ɗauka.
Jaridar Daily Trust ta ce da yake mayar da martani, daraktan yaɗa labarai na APC, Alhaji Bala Ibrahim, ya kare yadda jam’iyyar ta gudanar da mulki tare da nuna kokwanto kan manufar Lukman.
Wane martani APC ta yi?
Alhaji Bala Ibrahim ya nuna cewa Lukman ya kasance jigo a cikin shugabancin jam’iyyar tsawon shekara tara da ya ke suka.
"Ina girmama Lukman, amma idan haka yake tunani, yana buƙatar ya sake duba matsayarsa."
"Yana cikin masu tsara manufofi a cikin jam’iyyar, kuma idan APC ta gaza, to a fakaice Lukman ya yarda da gazawarsa, saboda yana cikin masu faɗa a ji."
"Idan har shekara tara na mulkin APC gazawa ne kamar yadda Lukman ke iƙirari, to shi ma dole ne ya karɓi alhakin wannan gazawar."
"Bayan haka, ya kasance mamba a kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) kuma ya taka rawa wajen bayar da shawarwari kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati."
- Alhaji Bala Ibrahim
Jigo a APC ya ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ba shugaban ƙasa Bola Tinubu muhimmiyar shawara.
Olatunbosun Oyintiloye ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta cire ƴan Najeriya daga cikin halin ƙuncin da suka tsinci kansu a ciki a halin yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng