"Na Yi Wasiyya Idan an Sace Ni" Sheikh Bello Yabo Ya Sha Alwashin Cafko Yan Bindiga

"Na Yi Wasiyya Idan an Sace Ni" Sheikh Bello Yabo Ya Sha Alwashin Cafko Yan Bindiga

  • Shahararren malamin musulunci, Sheikh Bello Yabo ya bayyana cewa a shirye ya ke ya taimaka wajen kawo karshen rashin tsaro
  • A daya daga cikin karatuttukansa, malamin ya ce ya na samun sakonnin masu garkuwa da mutane gare shi, kuma ko a jikinsa
  • Sheikh Bello Yabo ya kara da cewa shugabanni sun ci amanar yan bindiga, da ta al'ummar da su ke jagoranta da ta kawunansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Fitaccen malamin addinin musulunci, Bello Yabo ya bayyana cewa har yanzu tayin da ya yi wa gwamnatin tarayya kan ba shi dakaru a shiga daji a yaki yan ta'adda na nan. A daya daga cikin karatuttukan malamin, ya bayyana cewa sakonnin 'yan bindiga gare shi su na karasowa, kuma hakan ba zai tsorata shi ba.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano sun tashi da takaici, an tsinci jaririya a ƙarkashin tayar mota

Sheikh Yabo
Sheikh Yabo ya ce har yanzu tayin kamo yan bindiga na nan ga gwamnatin tarayya Hoto: Sheikh Bello Aliyu Yabo
Asali: Facebook

A bidiyon da wani mai amfani da shafin Facebook, Maje El-Hajeej ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Yabo ya ce yan bindiga sun turo masa da sako.

Sakonnin yan bindiga ga Sheikh Bello Yabo

Fitaccen malamin nan, Sheikh Bello Yabo ya ce ya na samun sakonnin wasu daga cikin yan bindiga na muradin garkuwa da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce daya daga cikin sakonnin, akwai dan bindigar da ya ce babu abin da ya ke fatan cimmawa a duniya irin ya sace Shehin malamin.

Sheikh Yabo ya kara da cewa akwai dan ta'addan da ya yi ikirarin matukar ya sace shi, kuma bai nemi a kawo kudin fansa a ba, zai daina sace jama'a.

Martanin Sheikh Bello Yabo ga yan bindiga

Sheikh Yabo ya ce yan bindiga sun samu lalatattun shugabanni, shi yasa su ke cin karensu babu babbaka.

Kara karanta wannan

'Sai na yi gaba da gaba da yan bindiga' Bello Yabo ya dauki zafi bayan masa gargadi

Ya bayyana cewa ya riga ya yi wasiyya, kar wanda ya biya ko sisi a matsayin kudin fansa idan an sace shi.

Sheikh Bello Yabo ya magantu masu zanga-zanga

A baya mun ruwaito cewa shehin Malamin addinin Islama, Sheikh Bello Yabo ya gargadi masu shirin gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Malamin ya ce su bi a hankali saboda masu kokarin kawo tarzoma, amma ya ce ba zai ce a yi ba, ko ya hana, kana ya shawarci malamai kan su daina tsoma baki a lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.