Awanni da Komawar 'Yan Kwankwasiyya APC, Gwamnati Ta Fara Rabon Shinkafa a Kano

Awanni da Komawar 'Yan Kwankwasiyya APC, Gwamnati Ta Fara Rabon Shinkafa a Kano

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya kaddamar da rabon shinkafar gwamnatin tarayya a Arewa maso Yamma
  • An ce tirela 19 na shinkafar ne za a raba a fadin Kano, yayin da gwamnatin za ta sayar da tirela 70 na shinkafa a farashi mai rahusa a jihar
  • Sanata Barau ya jaddada cewa shirin na daya daga cikin kudirin Shugaba Bola Tinubu na magance matsalolin tattalin arziki a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya kaddamar da rabon tallafin shinkafa ga jihohi bakwai na Arewa maso Yamma.

Da ya ke jagorantar kwamitin gwamnatin tarayya na rabon tallafin, Sanata Barau Jibrin ya kaddamar da shirin rabon a jihar Kano.

Kara karanta wannan

"Mutane za su wahala": Atiku ya yi adawa da shirin kara hajari, ya gargadi Tinubu

Sanata Barau ya fara rabon tallafin shinkafar gwamnati a Kano
Sanata Barau ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa Kano domin fara rabon shinkafar tallafi. Hoto: @barauijibrin
Asali: Facebook

An fara rabon shinkafar gwamnati

Sanata Barau ya jaddada cewa shirin na daya daga cikin kudirin Shugaba Bola Tinubu na kawar da matsalolin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa an kaddamar da shirin ba da tallafin shinkafar ne domin taimakawa al’umma a fadin jihohin Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto, Jigawa, da Zamfara.

Ya yi nuni da cewa kwamitin gwamnatin tarayya na rabon shinkafar ya kunshi wakilai daga jam’iyyun siyasa daban-daban domin tabbatar da adalci, daidaito da kuma amana.

An ba 'yan Kano tallafin shinkafa

Jaridar Tribune ta rahoto ministan noma da samar da abinci Abubakar Kyari ya ce jihar Kano za ta karbi tireloli 19 na shinkafa mai nauyin kilogiram 25 domin rabawa al'umma.

Ya kuma bayyana cewa ana sa ran nan ba da dadewa ba Kano za ta karbi tirela 70 na shinkafar da gwamnatin tarayya za ta sayar a farashi mai rahusa.

Kara karanta wannan

Babban hadimin Shugaba Tinubu ya ajiye aikinsa, ya jero dalilai masu ƙarfi

Kyari ya kuma kara da cewa a baya gwamnatin tarayya ta baiwa jihar Kano tirela 90 na kayan abinci da tirela 70 na taki domin rabawa jama'a matsayin tallafi.

'Yan Kwankwasiyya sun sauya sheka

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu jiga-jigan 'yan tafiyar Kwankwasiyya a Kano sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ta hannun Sanata Barau Jibrin.

Shugaban ‘yan kasuwar mai da iskar gas na jihar Kano, Hassan Nuhu Hassan da shugaban 'yan fim na Arewa, Salisu Muhammed Officer sun fice daga NNPP zuwa tafiyar Sanata Barau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.