Basarake Ya Rusa Kungiyoyin 'Yan Kasuwa, Ya Tilasta Sauke Farashin Kayan Abinci

Basarake Ya Rusa Kungiyoyin 'Yan Kasuwa, Ya Tilasta Sauke Farashin Kayan Abinci

  • Sarakunan gargajiya a garin Badagry a ranar Asabae sun dura kasuwar Agbalata domin aiwatar da umarnin da Sarkin Badagry ya bayar
  • An rahoto cewa Sarkin Badagry, Aholu Toyi I ya tilastawa 'yan kasuwar Agbalata sauke farashin kayan abinci da kayan masarufi
  • Rahotanni sun ce sarkin Badagry ya rushe kwamitocin 'yan kasuwar da ke kayyade farashin kayan abinci a kasuwar Agbalata, Badagry

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Badagry, Legas - Wasu sarakunan gargajiya sun mamaye kasuwar Agbalata domin aiwatar da umarnin da sarkin Badagry ya bayar na tilasta 'yan kasuwa sauke farashin kayan abinci.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da 'yan Najeriya ke kukan tsadar rayuwa da tsadar kayan masarufi yayin da kuma aka kara kudin man fetur.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi nasarorin da ya samu a China, ya bayyana amfanin kara kudin mai

Sarkin Badagry ya rusa kungiyoyin 'yan kasuwa, ya ba da umarnin sauke farashin kayan abinci
Legas: Sarkin Badagry ya dauki matakin karya fashin kayan abinci a kasuwar Agbalata. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Sarki ya tilasta sauke farashi

Sarkin Badagry, Aholu Toyi I, ya rusa kungiyoyin 'yan kasuwa da ke kayyade farashin kayan abinci da kuma cewa a sauke farashi a kasuwar Agbalata, inji rahoton The Guardian.

Mai martaba Aholu ya bayyana matakin rusa kungiyoyin 'yan kasuwar ne a ganawarsa da maza da mata na kasuwar Agbalata a fadarsa da ke Badagry.

Akaran wanda ya samu wakilcin Michael Onu-Osekan, Jengen na Badagry, ya ce babu wani kwamiti da ya isa ya tsayar da farashin kayan abinci da masu sayarwa ke kawowa kasuwar.

Ya kuma aika masu sanarwa da su yiwa ’yan kasuwar jagora zuwa wasu wurare hudu da ke cikin karamar hukumar domin yi musu jawabin matakin da aka dauka.

Sarakunan gargajiya sun zagaya kasuwa

Vanguard ta ruwaito Jenegen ya ce, sarakunan sun zo ne bisa umarnin Sarkin Badagry dangane da taron da ya gudanar a fadarsa kan farashin kayan abinci.

Kara karanta wannan

'Ba za mu iya rayuwa haka ba' An hada kai, an yi rubdugu ga Tinubu kan kudin mai

“Mun ji cewa wasu ‘yan kasuwa sun bijirewa biyan kudin shara, tsaro da sauran haraji, saboda umarnin fadar.
"Sakon shi ne kada 'yan kasuwar su sanya al'amura su tsananta ga mutanenmu, kada su tsawwalawa mutane fiye da kima da nufin samun riba mai yawa."

- Inji Michael Onu-Osekan.

Jihohi 10 mafi tsadar abinci

A wani labarin, mun ruwaito cewa rahoton farashin kayan abinci na NBS a Mayun 2024 ya nuna karuwar farashin da kashi 115.84 a 2023 idan aka kwatanta da farashin a Mayun 2023.

Kogi ke kan gaba a jihohin Najeriya mafi tsadar kayan abinci a daidai lokacin da take fama da kalubalen tsaro da kuma rigimar manoma da makiyaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.