An Rasa Muhalli da Dukiya: Jihohin Arewa da Ambaliyar Ruwa Ta Yiwa Barna a 2024

An Rasa Muhalli da Dukiya: Jihohin Arewa da Ambaliyar Ruwa Ta Yiwa Barna a 2024

Daga tsakiyar Yulin 2024 zuwa yanzu, mamakon ruwan sama da ake ci gaba da tafkawa ya haifar da ambaliya a sassan Najeriya, wanda ya jawo asarar rayuka, dukiya da kuma muhallai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A cewar NEMA, ya zuwa ranar 1 ga Satumba, 2024, ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 180; mutane 2,034 sun samu raunuka yayin da gidaje da gonaki suka lalace.

Dangane da sabon rahoton ambaliyar ruwa a 2024 da cibiyar ayyukan gaggawa ta kasa na NEMA ta fitar, Jihohi 28 da kananan hukumomi 140 a fadin kasar nan ambaliyar ta shafa.

Ambaliyar ruwa ta yi barna a sama da jihohi 7 na Arewacin Najeriya
Kano da wasu jihohin Arewacin Najeriya da ambaliyar ruwa ta yiwa barna a 2024. Hoto: Justin Sullivan
Asali: Getty Images

Girman barnar ambaliyar da ba a taba ganin irinsa ba ya kara jawo tabarbarewar yanayin tattalin arzikin kasar da kuma jefa mutane cikin makokin rasa 'yan uwansu.

Kara karanta wannan

Ku shirya: Gwamnati ta bayyana sunayen jihohi 7 da ambaliyar ruwa za ta yiwa barna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro wasu jihohin Arewa da ambaliyar ruwa ta yiwa mummunar barna daga farkon daminar bana zuwa yanzu:

1. Jihar Zamfara

Sakamakon ambaliyar ruwa da ta faru a jihar Zamfara, an ce sama da mutane 10,000 ne suka rasa matsugunansu yayin da gonaki da wasu kadarori na miliyoyin naira suka lalace.

An samu ambaliyar ruwan ne bayan da aka shafe makonni ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ƙaramar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

An kuma rahoto cewa kusan gidaje 2,000 a karamar hukumar Talata Mafara suka lalace musamman garuruwan Ruwan Gora, Morai da Makera.

2. Jihar Bauchi

A jihar Bauchi, ambaliyar ruwa ta shafi sama da dubunnan gidade a fadin kananan hukumomin Shira, Giade, da Katagum, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.

Jami’an hukumar SEMA sun ruwaito cewa:

Kara karanta wannan

Gini mai hawa 2 ya rikito a Kano bayan mamakon ruwa, mutane sun kwanta dama

“A Giade, sama da gidaje 300,000 ne ambaliyar ta lalata yayin da ta lalata gidaje sama da 400,000 a karamar hukumar Shira. Ambaliyar ta rusa dubunnan gidaje a Katagum."

3. Jihar Sokoto

A jihar Sokoto, ambaliyar ruwa a ranar 17 ga Yuli, 2024, ta raba akalla mutane 1,664 da muhallansu a cikin garuruwa hudu na karamar hukumar Gada.

An rahoto cewa ambaliyar ta lalata gonaki da jawo rasa rayuka, inda Dantudu, Balakozo, Gidan Tudu, da Tsitse na cikin garuruwan da iftila'in ya fi yiwa barna

4. Jihar Jigawa

A cewar kafofin yada labarai, ya zuwa ranar 24 ga watan Agusta, ambaliyar ruwa ta kashe akalla mutane 33, mutane 44,000 kuma sun rasa muhallansu, sannan ta lalata gidaje 7,800 a jihar Jigawa.

Sai dai shugaban hukumar SEMA a Jigawa, Dakta Haruna Mairiga ya shaidawa Legit cewa an rasa gidaje akalla 7,060 ne a jihar yana mai nuna fargabar sake faruwar wata ambaliyar.

Kara karanta wannan

Kano: Ambaliya ta halaka mutum 31, gidaje 5,280 sun rushe a ƙananan hukumomi 21

Gwamnatin Jigawa ta ce jihar ba ta yi tsammanin ambaliyar ruwa a watan Agusta ba amma ayyukan titunan gwamnatin tarayya wanda ya toshe hanyoyin ruwa ne ya jawo matsalar.

5. Jihar Adamawa

Ofishin OCHA na Majalisar Dinkin Duniya ya rahoto cewa, mutane 45 da suka bace, mutane 10,264 da suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliya a Adamawa.

Rahoton ya ce ambaliyar ta shafi mutane 12,583 yayin da kuma gidaje 298 suka ruguje sakamakon ambaliyar a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

6. Jihar Borno

A ranar 22 ga Yuli, 2024, ambaliyar ruwa ta yi sanadin barna a wasu sansanonin 'yan gudun hijira da ke a kananan hukumomin Dikwa da Mafa (LGAs) na jihar Borno.

Cibiyar kididdiga kan 'yan gudun hijira ta duniya, DTM ya rahoto cewa ambaliyar ta lalata matsuguni 265 wanda ya shafi mutane 4,444 daga gidaje 906 da suka rasa muhallansu.

Kara karanta wannan

Yan sandan Kano da Kaduna sun hada kai, an ceto budurwa da ta kwana 35 hannun miyagu

Mutanen da abin ya shafa sun hada da mata 600, maza 491, da yara 1,460.

7. Jihar Kano

Mun rahoto cewa iftila'in ambaliyar ruwa ya yi sanadin mutuwar mutane 31 tare da lalata gidaje 5,280 a ƙananan hukumomi 21 na jihar Kano.

Babban sakataren hukumar ba da agajin gaggawa ta Kano (SEMA), Isyaku Kubarachi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da yan jarida ranar 4 ga Satumbar 2024.

Isyaku Kubarachi ya bayyana cewa ambaliyar ruwan ta shafi akalla mutane 31,818, sannan ta lalata amfanin gonakin jama'a da suka kai kimanin 2,518.

Ambaliya ta shafi Neja, Kebbi

A wani labarin, mun ruwaito cewa ambaliyar ruwa ta lalata amfanin gonakin al'ummomi da dama a karamar hukumar Argungu da wasu yankunan na jihohin Kebbi da Neja.

Shugaban sashin hulɗa da jama’a na hukumar N-HYPPADEC, Nura Wakili ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar 27 ga Agustar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.