CBN Ya Yi Gum Ana Rade Radi Gwamna da Mataimakansa Sun Sayo Motocin N10bn

CBN Ya Yi Gum Ana Rade Radi Gwamna da Mataimakansa Sun Sayo Motocin N10bn

  • An zargi babban bankin Najeriya da kashe makudan kudi domin sayen motocin gwamna da sauran mataimakansa
  • Akwai jita-jita cewa bankin na CBN ya batar da N10bn domin sayen wasu manyan Lexus da harsashi bai iya ratsa su
  • Bincike ya nuna motocin ba za su kai yadda ake yadawa ba, amma bankin CBN bai iya karyata zancen ba har yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Babban bankin Najeriya watau CBN ya yi tsit game da zargin da ake yi cewa gwamnoninsa sun saye wasu manyan motoci.

Jita-jita na yawo cewa Olayemi Cardoso da sauran mataimakan gwamnonin bankin CBN sun saye motocin da harsashi bai iya ratsa su.

Gwamnan CBN
Gwamnan CBN, Yemi Cordoso a taron Afrika Hoto: @cenbank
Asali: Twitter

Duk da yadda labarin yake ta yawo, Daily Trust ta kawo rahoto cewa babban bankin na CBN ya yi gum a game da wannan rade-radin.

Kara karanta wannan

An soki Barau Jibrin kan karbar mutane zuwa APC alhali ana kukan kuncin rayuwa

Daily Nigerian ta fara kawo labari cewa gwamnonin bankin sun saye motar Lexus LX 600.

An zargi bankin CBN da facakar kudi

Shugaban cibiyar CISLAC, Mallam Auwal Musa Rafsanjani ya soki zancen inda ya zargi shugabannin bankin na CBN da facaka da kudi.

Mallam Auwal Musa Rafsanjani ya bukaci gwamnatocin tarayya da jihohi su tashi tsaye wajen yaki da barna da dukiyar al’ummar kasar.

CISLAC ta kara da zargin Yemi Cordoso ya saye motoci 20 wanda kowace ta tashi a kan N85m, sannan ya kara kudin gida zuwa N1bn.

Idan zargin ya tabbata, an ware kudin ne duk da suna zama a gidajen gwamnati yayin da mafi yawan mutane ke kukan kunci.

Gwamnan CBN da mataimaka sun saye motoci?

Motocin da ake magana (Lexus LX 600 2023) sun kai N260m, farashin gaba dayansu zai kai N1.5bn akasin N10bn da aka rahoto a baya.

Kara karanta wannan

Bayan kara kudin mai: Gwamnati ta fadi lokacin da fetur zai wadata a fadin Najeriya

Daily Post ta ce mataimakan gwamnonin CBN sun samu mota guda sai gwamnan ya tashi da biyu domin aiki a Legas da birnin Abuja.

Har yanzu CBN bai iya karyata labarin a shafinsa na yanar gizo ko a dandalin X ba, kuma kakakinsa Sidi Hakama ta gaza cewa komai.

Mataimakan gwamnonin bankin CBN

A Satumban bara aka ji labarin yadda tsohon Hadimin Nasir El-Rufai ya shiga cikin mataimakan gwamnan bankin CBN a Najeriya.

Mataimakan gwamnonin su ne Philip Ikeazor, Emem Nnan Usoro, Bala Bello da Muhammad Sani Abdullahi da aka nada a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng